A fitar da ’yan takara ta hanyar zaben fidda-gwani – danragi
Mai neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar kujerar Gwaman Jihar Neja Alhaji Saleh Sahabi darangi ya bukaci a bar kowane dan takara ya gwada sa’arsa a zaben fidda-gwani, maimakon a janye wa mutum daya. Alhaji Saleh Sahabi darangi ya fadi haka ne a ganawarsa da wakilinmu sakamakon rade-radin da ake yayatawa cewa Gwamna […]
Mai neman Jam’iyyar PDP ta tsayar da shi takarar kujerar Gwaman Jihar Neja Alhaji Saleh Sahabi darangi ya bukaci a bar kowane dan takara ya gwada sa’arsa a zaben fidda-gwani, maimakon a janye wa mutum daya. Alhaji Saleh Sahabi darangi ya fadi haka ne a ganawarsa da wakilinmu sakamakon rade-radin da ake yayatawa cewa Gwamna Mu’azu Babangida na mara wa daya daga cikin masu neman takarar. dan siyasar ya ce mutanen da suka fito domin neman jam’iyyar ta tsayar da su takara, mutane ne da suke da kwarewa a fannonin rayuwa, don haka duk wanda ya samu nasara a cikinsu yana iya jan ragamar jihar. Ya ce jama’a za su fi gamsuwa da zaben fitar da gwani kowa ya gwada sa’a kuma a kwatanta gaskiya kowa yana gani. Alhaji Sahabi Saleh ya ce da dadewa jama’a suka yi ta kai masa caffa kan bukatar ya shiga takara a karkashin Jam’iyyar PDP. Ya ce, ya zagaya kananan hukumomi da dama da wasu gundumomin jihar. Kuma duk inda suka je jama’a na maraba da su. Ya ce ya lura akasarin al’umomin yankunan karkara na fama da rashin muhimman ababen more rayuwar da suka hada da hanyoyi da asibitoci da makarantu. Alhaji Sahabi Saleh ya jinjina da wa shugabannin Jam’iyyar PDP a dukkan matakai kan nasarar da ta samu, inda ya ce kowa na da gudunmawar da ya bayar wurin kafa jam’iyyar tun daga 1998.