A fito da harajin rijiyar burtsatse

Edita a ba ni dama in yi kira ga ’yan Majalisa da su kafa doka, wadda za ta kula da rijiyar burtsatse (borehole) a cikin garuruwan Najeriya. Yanzu abin ya zama kamar gasa a wajen mutane masu hannu da shuni, wajen gina rijiyar burtsatse a cikin gidajen su. Yin hakan yana kawo tsotsewar rijiyoyin al’umma […]

A fito da harajin rijiyar burtsatse
A fito da harajin rijiyar burtsatse

Edita a ba ni dama in yi kira ga ’yan Majalisa da su kafa doka, wadda za ta kula da rijiyar burtsatse (borehole) a cikin garuruwan Najeriya. Yanzu abin ya zama kamar gasa a wajen mutane masu hannu da shuni, wajen gina rijiyar burtsatse a cikin gidajen su. Yin hakan yana kawo tsotsewar rijiyoyin al’umma a cikin birane, musamman a Arewacin Najeriya. Duk da cewa cewa gwamnati ta gaza wajen bada tsaftataccen ruwan sha ga al’umma, duk da haka ya zama dole a kafa dokar hana yin rijiyar burtsate a cikin gidaje. Gwamnati na iya sanya haraji ga masu rijiyoyin, tare da wajibta yankar kati a kan duk mai son yin burtsatse a gidan shi. Hakan zai kawo zaman lafiya a cikin jama’a da kawar da zargi da jin kyashi a tsakanin makwabta.

Kwamared Abdulbaki Jari Katsina 08035424321, Lay out Katsina.

Kira ga CBN
Ina kira ga Babban Bankin Najeriya, wato (C B N) da cewa, wannan sabuwar Naira 100 da aka buga ba ta da ingancin ta da, don tuni ta fara lalacewa, jama’a sun fara kin karbarta. Ko dai a bar mana ta da, ko a sake mana ta leda, kamar Naira 50 da 20. Daga Isah sani mai Arsenal Garkon Alli, Jihar Jigawa.08062332784.

Godiya ga Editan Aminiya
Godiya ta musamman ga Editan Aminiya domin bai wa talakawa damar fadin ’yanci albarkacin bakinsu, ina matukar jin dadin karanta jaridarku tare da fatan Allah ya ba ku kwarin gwiwar aiwatar da ayyukanku, ameen. Daga Nasiru Jafaru Shika, Jihar Kaduna.

Mun gamsu Namadi
Assalamu alaikum Aminiya, hakika ina kalamai masu faranta rai ga al’ummar Annabi, tunda ya ce sadaka ce, kalaman Alhaji Namadi Sambo da ya yi wa al’ummar Najeriya ta kafafen watsa labarai, mun ji kuma mun gamsu da fatan za su cika alkawari kamar yadda suka dauka na mika mulki ga sabuwar gwamnati da zarar an gudanar da zabe a cikin kwanciyar hankali da lumana. Allah ya ida nufi. Daga Alhaji Umar Foreber Gashua 08108003333.

PDP ta zama tarihi
Hakika yadda muhimman mutane irinsu: Olusegun Obasanjo ke cigaba da ficewa daga jam’iyyar PDP, wata babbar alama ce da ke kara nuna cewa, jam’iyyar PDP ta kusa zama tarihi a Najeriya. Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja. 08060353382.

Mu dage da addu’a
Ina kira ga talakawan Najeriya da mu dage da addu’a don neman Allah ya kawo mana karshen mulkin zalunci irin na jam’iyyar PDP. Daga Abubakar Umar Kofa 08065746051.

Jaje ga Jasawa
Edita ina mai neman alfarma da a ba ni izini in mika wa al’umman Jos ta’aziyar ’yan uwa da suka rasu a tashin bama-bamai da ya auku ranar Alhamis din da ta gabata. Da fatan Allah ya jikansu, ya kuma gafarta musu amin. Daga Dauda Shehu Masalla, Anguwar Rogo Jos.

Ta’aziyya ga Jasawa
Salam Edita Ina son ka mika min ta’aziyata ga jama’ar Jos. Da fatan Allah ya gafarta wa ’yan uwanmu da bom ya rutsa da su amin. Daga Yusif Lamba One Jos, ’Yan doya. 07061957888.

Ta’aziyyar Sheikh dandume
Allahu Akbar, ina mika sakon ta’aziyata ga ’ya’ya da ’yan uwa da masoyan babban malamin nan da ya rasu ranar Jumma’a sheik m Halilu dandume Allah ya jikansa da rahama amin. Daga Muhammad B. Alhussaini Madallah 07034560742.

Ga Matawallen Sakkwato
Salam Aminiya ku isar min sakon gaisuwa ga Matawallen Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, da kuma shugaban kungiyar Matasan Matawalle, wato “Matawalle Youth Organisation,” da ke Lugu Area Wamakko, Alhaji Kabiru Turakin Lugu. Gaba dai, gaba dai jam‘iyyar APC. Daga Muhammad Sirajo Hamidu Lugu bictoria Island, Jihar Legas.

Aminiya a yafe mini
Salam Edita, wai don Allah me na yi muku ba kwa buga sakonnina ne? Ina fata za ku yafe mini. Daga Abdul Usman Abuja. 08133844064.

Kira ga ’yan siyasa
Salam Edita ina maka fatan alkairi. Don Allah ka isar mini da sakona wajen ’yan siyasar kasata, Najeriya da su daina amfani da matasa wajen bangar siyasa; wajen aiki da su; wajan biyan bukatunsu, bayan ba za su sa ’ya’yansu ba. To, matasa kalubale gare ku. Daga Bashir Sa’idu dan kwambo, Maigora, Jihar Katsina.

Jama’a a karbi kati
Assalam Edita. Wallahi in har muna son ceton kasar mu, tare da kafa gwamnatin adalci da ci gaba a Najeriya, to ya zamo dole komai wahala, komai tsanani, mu daure mu mallaki katin zabe, kamar yadda na yi ta naci, har sai da na karbi nawa. Domin shi ne bindigarmu ta harbe azzaluman shugabanni a ranar zaben a ranar 28.3.2015 insha Allahu. Jama’a a guji kwadayi a ran zabe. Daga MK Ibrahim Zeze, Hausa Layi Legas.

APC ce cancanta
Ina kira ga al’ummar Najeria.Idan aka ce a zabi cancanta a siyasar Najeriya, shi ne a zabi jam”iyar APC da duk ’yan takarar ta, domin su ne suka cancanta. Daga Isma’il Alkyabba Funtuwa.

Taya murna ga Shagari
Salama Ina taya tsohon Shugaban kasa Najeriya a jamhuriyya ta biyu, Alhaji Shehu Shagari turakin sokoto murna cika shekara 90 da haihuwa. Daga Bello Dandin Mahe Suleja.

Mu dage da addu’a
Salam. Ina kira ga ’yan uwana ’yan Najeriya, Musulmi da Kirista da mu ci gaba da addu’a kan dage zabe da aka yi, in makirci aka kulla mu roki Allah ya sauya mana zuwa alheri, don babu abin da ya gagari Allah. Daga Isah Dilwaala Abuja.

Kira ga ’yan Najeriya
Ediata ka isar da sakona ga ’yan Najeriya, mu hada kai mu zabi wanda zai yi mana adalci, kamar Janar Muhammad Buhari na jam’iyyar APC. Daga Ibrahim Sudan 07087328577.

Kira ga ’yan siyasa
Sako ga ’yan siyasa don Allah ku fada wa ’yan siyasa su daina kalaman sharri ga ’yan adawa, don neman biyan bukatarsu. Mu kuma masu zabe, mu duba cancanta. Daga Bashir Mai chemist Damau Kubau, Jihar Kaduna 08031513429.