A fito da kudin da aka tara don ’yan gudun hijira – Sarkin Musulmi
Shugaban majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya koka ga halin kuncin da ’yan gudun hijira ke ciki a yakin Arewa, musamman yankin Arewa maso gabas mai fama da rikicin Boko Haram, inda ya kalubalanci gwamnonin Arewa da su tabbatar da sun gano inda biliyoyin nairori da aka tara domin tallafa wa […]
Shugaban majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya koka ga halin kuncin da ’yan gudun hijira ke ciki a yakin Arewa, musamman yankin Arewa maso gabas mai fama da rikicin Boko Haram, inda ya kalubalanci gwamnonin Arewa da su tabbatar da sun gano inda biliyoyin nairori da aka tara domin tallafa wa ’yan gudun hijiran suka fada.
A cewarsa, akwai bukatar a gano inda wadannan kudaden suke domin a taimaka wa ’yan gudun hijiran da su, domin manufar tara kudin ke nan.
Sultan Sa’ad ya yi wannan furuci ne a wajen taron sarakunan Arewa da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata a Kaduna.
Ya ce kudin an tara su ne saboda inganta jin dadin ’yan gudun hijira, amma a yanzu irin labaran da ake yadawa a shafukan jaridu abin bakin ciki ne. “Saboda haka akwai mahimmanci sosai a tabbatar da an raba wadannan kudade ta hannun gwamnoni. A duk lokacin da muka hadu da shugabanninmu na siyasa mukan fada masu gaskiya, kuma abin da muke yi ke nan a nan, kuma za mu cigaba da shawartarsu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, domin jin dadi da cigaban al’ummarmu, musamman a yankin Arewa. Mun tabbatar da cewa idan har aka kawo karshen matsalolin Arewa, muna da yakinin Najeriya za ta zauna lafiya. Saboda haka ne za mu tattauna matsalolin Arewa da Najeriya baki daya a taron namu.’’
Ya kara da cewa, “Za mu tattauna matsalolin ’yan gudun hijira a yankin Arewa maso gabas. Mutanen na cikin wahala kuma biliyoyin nairori aka amsa ko kuma aka ware domin kulawa da ’yan gudun hijira, abin da muke ji a kafafen yada labarai babu dadin ji. Saboda haka ya dace a raba wadannan kudade domin jin dadin ’yan gudun hijiran nan. Dole ne a yi amfani da kudaden, saboda idan mutum ya rigaya ya mutu ba ya bukatar wani abu sai addu’a, saboda haka tun da ’yan gudun hijiran na raye sai mu taimaka masu, saboda ’yan uwanmu ne maza da mata. Muna rokon gwamnonin da su dauki batun da mahimmanci, ta hanyar sanar da shugaban kasa domin a saki wadannan kudade, domin ina cikin wadanda suka halarci taron da aka yi domin tara wadannan kudi a lokacin gwamnatin da ta shude, saboda kulawa da ‘yan gudun hijira,” inji shi.
Sultan din ya kuma nuna damuwarsa game da ikirarin da matasan MASOB ’yan kudu maso gabas ke yi na neman kasar Biafara, inda ya ce akwai ’yan kabilar Ibo da ke zaune a Arewa masu yawan gaske kuma a nan suke sana’oinsu, domin ba su da inda za su tafi, saboda haka ya ce majalisar sarakunan za ta kafa kwamitin da zai ziyarci yankin na kudu maso gabas domin ganawa da sarakunansu a kan wannan batu.
Shi kuwa Gwamnar jahar Adamawa Jibrila Bindow, kira ya yi ga sarakunan da su taimaka wajen hana ’yan gudun hijira na bogi yin tururuwa zuwa cikin sansanonin ’yan gudun hijira da ke kasar nan.