A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha

Ta ce mijinta shaida ne cewa tun shekarar 2023 Shugaban Majalisar Dattawan yake bibiyar ta domin yin lalata da amma ta ki ba shi haɗin kai

A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha

Sanata Natasha Akpoti ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio da neman yin lalata da ita.

’Yar Majalisar Dattawa daga Jihar Kogi ta bayyana cewa mijinta ma shaida ne a kan yunkurin Akpabio ne yin lalata da ita.

A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a, Sanata Natasha ta ce tun da ta ki amincewa da buƙatar Shugaban Majalisar ya kafa mata ƙahon zuƙa.

A makon da ya gabata ne Natasha ta yinwa Akpabio wankin babban bargo a zauren Majalisar bayan ya sauya mata kujera ba tare da tuntubar ta ba.

Ya ba da umarnin ne bayan da ’yan majalisar suka kada ƙuri’ar amincewa da hakan, domin tabbatar da dokokin zauren Majalisar.

Daga bisani ya tura lamarin ga kwamitin ladabtarwar majalisar ta gudanar da bincike tare da gabatar da rahoto cikin makonni biyu.

Ana cikin haka ne ’yar majalisar ta maka shi a kotu tana neman diyyar Naira biliyan 100.03.

A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a, Sanata ta ce, tana da hujjoji da hotunan saƙonnin da ya aika mata.

’Yar Majalisar ta ce Akpabio ya sha kiran ta ta manhajar WhatsApp, sa’annan ta buƙaci Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta bibiyi wayar da suka yi domin gano gaskiya.

Ta bayyana cewa ta sha neman gabatar da kudiri kan Masana’antar Mulmula Karfe na Ajaokuta a zauren Majalisar amma Akpabio yana kin sanya batun a jerin abubuwan da za a tattauna a majalisar.

Ta ce daga bisani bayan ta nuna damuwarta wasu sanatoci suka bukaci ta je ta yi masa magana saboda muhimmancin masana’antar.

Ta ce, da ta yi masa magana sai ya ce, “Sanata Natsaha, a matsayina ba shugaban majalisar nan, Ni ke da wuƙa da nama. Ya kamata ki ba ni kulawa, domin idan kika kuka da ni za ki samu alherai masu yawa.”

Ta ce, ko da ta bayyana masa cewa ba ta fahimta ba sai ya ce, “ya rage naki.”

Ta ce, “wannan abun da ke faruwa da ni daidai yake da na malamin da ke wahalar da ɗalibarsa saboda ta ƙi kwanciya da shi.”

Ta bayyana cewa tun a shekarar 2023 Akpabio ya fara yi mata wannan mummunan tayi a lokacin da ita da mijinta suka ziyarce shi domin taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Ta ce “yana rike da hannuna muna zagayawa yana nuna mana cikin gidansa, mijina na biye da mu, sai ce zai soma ce na zo gidansa mu huta.

“Mijina da ke biye da mu ya ji maganar, saboda haka ya hana mu tafiya ƙasar waje ni kadai ko in yi tafiya da Akpabio shi kadai.”

Zuwa yanzu dai babu wani martani daga Akpabio gane da wannan zargi, a yayin da batun ke ta yawo a kafofin sada zumunta.