Ni da mahaifiyarmu muna kallo aka zare ran kanina —Dangote
A kan idon Dangote da mahaifiyarsu da ’ya’yan mamacin aka dauki ransa a gadon asibiti.
Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana matukar kaduwarsa kan yadda kaninsa ya rasu a gabansa.
Dangote ya bayyana haka ne a yayin da yake karbar gaisuwar ta’aziyya daga Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu.
Ya shaida wa Tinubu a gidansa da ke Kano cewa, rasuwar “Da zafi sosai saboda a gabanmu ya rasu, ni da mahaifiyarmu da kuma ’ya’yansa.”
Dangote ya ce abin da ya fi ban takaici shi ne suna tare da marigayi Sani a gadon jinyarsa, likitoci suka shaida musu cewa cikin sa’a daya ransa zai yi halinsa.
Kanin nasa, Sani Dangote, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote ya rasu ne ranar Lahadi a Amurka, inda ake jinyar sa saboda cutar kansa da ya yi fama da ita.
An sallace shi ranar Laraba a Kofar Kudu, Fadar Sarkin Kano, bayan an dawo da gawarsa a safiyar ranar.