A gafarta min gazawata – Jonathan

A nasa jawabin Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya ce babu wata gwamnati ciki har da tasa da take cikakkiya, don haka ya bukaci ’yan Najeriya su gafarta masa kan duk irin kuskuren da ya yi. Ya ce: “Babu wani tsari da yake cikakke. Duk wani tsari na mutum yana da nau’i na gazawa. […]

A gafarta min gazawata – Jonathan

  • A nasa jawabin Shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan ya ce babu wata gwamnati ciki har da tasa da take cikakkiya, don haka ya bukaci ’yan Najeriya su gafarta masa kan duk irin kuskuren da ya yi.

  • Ya ce: “Babu wani tsari da yake cikakke. Duk wani tsari na mutum yana da nau’i na gazawa. A cikin shekara takwas da muka yi a nan zan dauki lokacin a matsayin daya, domin daukakata daga Mataimakin Shugaban kasa zuwa Shugaban kasa ta bi mataki-mataki ne kuma cike da takaddama. Kuma a harharde take ta yadda ba za a iya jan layi a tsakani ba. Domin lokacin da Shugaban kasa ke fama da rashin lafiya, ni nake tafiyar da kasar na wani lokaci, tun ma kafin kaddara ta sa a nada ni Shugaban kasa na riko. Sannan na zama Shugaban kasa na gudanar da zaben shekarar 2011 na samu nasara, don gudanar da mulki na shekara hudu a matsayina na zababben Shugaban kasa.”
    Jonathan ya ci gaba da cewa: “Don haka ina wannan wuri na tsawon shekara takwas, gaskiyar magana mutum tara yake. Kuma hakika mun yi wasu abubuwa da ba su kamata mu yi ba, amma ba da gangan ba ne. Don haka duk wanda muka saba masa ba da gangan ba ne, yanayi ne na harkar shugabanci. Saboda haka muna rokon wadannan mutan su yafe mana, muna jin mun yi bakin kokarinmu. Kuma za ka iya yin bakin kokarinka amma abokanka su kasa fahimtarka. Yau muna maganar sauka daga mulki. Ubangiji ne kawai Ya san dalilin da al’amura suke gudana haka.”
    Daga nan sai ya gode wa dukkan wadanda suka tallafa masa a lokacin mulkinsa inda ya ce: “Mun zo a matsayin Mataimakin Shugaban kasa ni da mata ta, yanzu muna barin mulki a matsayin tsohon Shugaban kasa da tsohuwar matar Shugaban kasa. Mun samu nasara ne ta tallafinku. Don haka ina godiya ga limamin cocin fadar Shugaban kasa da mukarrabansa da fastoci da matansu. A shekara takwas muna da cikakken dalili na nuna godiya ga Ubangiji. Kowane mutum yana da abin da ya fi mayar da hankali a kai. Kuma ina da yakinin duk mutanen da suka samu kansu a matsayin shugabanci suna da abin da suka fi mayar da hankali a kai. Babu wani shugaban gwamnati a matakin tarayya ne ko yanki da zai iya yin komai. Sai dai a lokacin da z aka sauka daga mulki kakan so ka yi wani abu da za ka nuna eh, na zauna a nan. Limamin ya ce, babau abin da yake cikakke; idan ka jira komai ya cika ba za ka iya yin komai ba.”
    Shugaba Jonathan ya kara da cewa: “Ranar 24 ga Mayu ce ya kamata ta kasance na yi addu’armu ta karshe a nan. To amma a ranar za mu tafi Cibiyar Kiristoci ta kasa don addu’o’in mika mulki. Don haka ni da matata wannan ne ranar karshe ta addu’armu a nan.”
    Shugaba Jonathan ya ce aikin Shugaban kasa aiki ne mai cike da kalubale, kuma bai amince cewa sai mutum yana gwamnati ne kawai zai samu daukaka ko cin nasara ba. Ya ce: “Hakika ban amince cewa sai in kana gwamnati ne kawai za ka iya yin wasu abubuwa; ko a wajen gwamnati za ka iya yin abubuwa da yawa. Manyan masu kudi na duniya ba su ma taba aikin gwamnati ba. dangote bait aba shiga gwamnati ba, don haka ba sai ka shiga gwamnati z aka zama mai kudi ba. Bill Gates bai taba shiga gwamnati ba, don haka abubuwa da yawa na faruwa a wajen gwamnati, abin da ake bukata daga gare mu mu sadaukar tare da ci gaba da nema. Ni da matata hakika muna son ku.”