A gaggauta kuɓutar da sauran ɗaliban jami’ar da aka sace a Gusau — Tinubu

A shirye gwamnatina take wajen kare duka ’yan Najeriya.

A gaggauta kuɓutar da sauran ɗaliban jami’ar da aka sace a Gusau — Tinubu

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su kuɓutar da sauran ɗalibai mata na Jami’ar Tarayya da ke Gusau a Jihar Zamfara da masu garkuwa da mutane suka sace.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban da aka yi ranar Juma’a, yana mai cewa wannan abu ne na rashin tausayi da imani kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Tinubu wanda ya jajanta wa iyalan waɗanda aka sacen, ya tabbatar da cewa a shirye gwamnatinsa take wajen kare duka ’yan Najeriya, yana mai alƙawarta cewa za a yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ɗaliban.

Haka kuma shugaban ya ce Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da bayar da kariya ga makarantu kasancewarsu cibiyoyin bayar da ilimi da ci gaban al’umma.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Juma’a da daddare ne wasu ’yan bindiga ɗauke da makamai suka dirar wa ɗakunan kwanan ɗaliban da ke unguwar Sabon-Gida tare da sace ɗalibai galibinsu mata, sai dai daga baya rahotonni sun ce an kuɓutar da wasu daga cikinsu.

Gyaran TCN ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a Abuja

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024