A gaggauta ceto ɗaliban da aka sace a Kaduna — Tinubu

Ba zan lamunci duk wani uzuri ba har sai an ceto waɗanda da aka yi garkuwa da su.

A gaggauta ceto ɗaliban da aka sace a Kaduna — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da satar ɗalibai a Jihar Kaduna da ’yan gudun hijra a Jihar Borno tare da bayar da umarnin a gaggauta ceto su.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale a wata sanarwa ya ce shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta ceto ɗaliban da ’yan gudun hijirar da kuma hukunta masu hannu a lamarin.

Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar ranar Alhamis ce ’yan bindiga suka yi garkuwa da ɗaliban firamare da na sakandare 287 a makarantarsu da ke ƙauyen Kuriga a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Haka kuma, a makon nan ne mayaƙan Boko Haram suka yi awon gaba da wasu mata 319 ‘yan gudun hijira a garin Ngala da ke Karamar Hukumar Gambarou Ngala ta Jihar Borno.

Sanarwar da Ngelale ya fitar a wannan Juma’ar ta nakalto Tinubun yana cewa “Shugabannin hukumomin tsaro sun yi min bayani a kan abin da ya faru a Borno da Kaduna kuma ina da yaƙinin cewa za a ceto su.”

“Na samu bayanai daga manyan jami’an tsaro game da hare-hare biyu da aka kai a Borno and Kaduna, kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa za a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya ƙara da cewa, “Na umarci jami’an tsaro da na leƙen asiri su gaggauta kuɓutar da waɗanda aka sace sannan su tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki.”

Shugaba Tinubu ya ce ba zai lamunci duk wani uzuri ba har sai an ceto yaran da aka yi garkuwa da su.

Ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa, tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi duk abin da ya dace domin dawo da ’yan uwan su.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo