A gaggauta gyara tsarin tsaron, inji Buhari
Mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, mai ritaya ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nuna rashin jindadin kan kara lalacewar tsaro a Najeriya. Monguno, da yake magana da ‘yan jarida kan abun da suka tattauna bayan kammala taronsu da shugaban kasa, ya ce Shugaba Buhari a shirye […]
Shugaban Kas Muhammadu Buhari
Mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, mai ritaya ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nuna rashin jindadin kan kara lalacewar tsaro a Najeriya.
Monguno, da yake magana da ‘yan jarida kan abun da suka tattauna bayan kammala taronsu da shugaban kasa, ya ce Shugaba Buhari a shirye yake ya gyara tsarin tsaron na kasa.
Ya Kuma ce sun tattauna matsalolin fasakwaurin kwayoyi and shaye-shaye da matsalolin tsaro a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Monguno ya ce shugaban kasa ya kara nanata wa shugabannin tsaron cewar kokarin da suke yi ba is a ba.
Ya ce kuma maganar karin kaimin da soji a fagen fama abu ne da ya shafi harkar gudanarwa saboda haka Ministan Tsaro, Bashir Magashi, “Yana kokarin yin wani abu” da zai samar da sabon salo ga jami’an tsaron.
Ya ce kuma ana danganta rashin tsaron da ake fama da shi da matsalar shaye-shayen da ake fama da ita.
“Shaye-shaye ke kara rururta matsalolin tsaro da ake fama da su a kasar nan”, inji shi.
Monguno ya ce Shugaban Buhari a shirye yake ya magance matsalolin tsaro duk da rashi fidda rai da yan Najeriya su ka yi.