A gaggauta hukunta masu hannu a bacewar Janar Alkali – Kungiyoyin Musulmi

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa (JNI), sun bukaci Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojin Najeriya su tabbatar sun hukunta duk wanda yake da hannu wajen bacewar Janar Idris Muhammad Alkali a hanyar garin Du da ke Jihar Filato. Manyan kungiyoyin Musulmin biyu, sun bayyana haka ne […]

A gaggauta hukunta masu hannu a bacewar Janar Alkali – Kungiyoyin Musulmi

Babban Sakataren JNI, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu a yayin da yake jawabi

Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta Kasa (JNI), sun bukaci Gwamnatin Tarayya da Rundunar Sojin Najeriya su tabbatar sun hukunta duk wanda yake da hannu wajen bacewar Janar Idris Muhammad Alkali a hanyar garin Du da ke Jihar Filato.

Manyan kungiyoyin Musulmin biyu, sun bayyana haka ne a taron manema labarai da suka kira a lokuta daban-daban a ranar Litinin da ta gabata a Kaduna, inda suka bukaci a dauki matakin gaggawa game da batun bacewar Janar Alkali da kuma sauran kashe-kashen da ake yi a Filato.

Babban Sakataren Majalisar Koli, Dokta Nafi’u Baba Ahmed ya bukaci sojoji su tabbatar sun binciki dukan kududdufan da ke kauyen Du domin sanin abubuwan da suke cikinsu.

Ya ce zanga-zangar da matan kabilar Berom da ke kauyen  Du suka yi lokacin da sojoji ke kokarin bincike a kududdufin, kokari ne na hana sojoji gano irin barnar da suka dade suna aikatawa a yankin.

“Wannan ya sa muke ganin akwai bukatar a binciki dukan kududdufan da suke yankin domin sanin abin da ke ciki. Kuma duk wanda aka samu yana da hannu cikin wadannan kashe-kashe da suka dade suna faruwa a garuruwan Berom a hukunta shi komai matsayinsa,” inji shi.

“Muna ganin akwai sakacin jami’an tsaro musamman ’yan sanda da SSS da sauransu da ke aiki a kananan hukumomin Barikin Ladi da Riyom da Jos ta Kudu, inda yawancin kashe-kashen suke faruwa. Ta yaya za a ce irin wadannan abubuwa na faruwa amma ba su sani ba. Saboda haka akwai bukatar gwamnati ta fadada bincike domin gano sauran mutanen da aka kashe. Janar Alkali mutum ne mai kima da gaskiya, don haka dole a gano masu hannu a bacewarsa don a hukunta su. Wannan majalisar tana kira a biya diyya ga ’yan uwan duk wanda aka gano gawarsa a cikin wannan kududdufi domin rage musu damuwa a zukatansu,” inji shi.

Majalisar ta kuma zargi Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) da wasu kafafen wasa labarai kan yin shiru a kan batun da kisan gillar da kabilar Berom suka dade suna yi wa Musulmi a yayin wucewa ta kauyukansu.

Shi ma Babban Sakataren JNI, Sheikh Khalid Abubakar Aliyu ya ce abin bakin cike ne yadda kungiyoyin kare hakkin jama’a na duniya da na cikin kasa, suka ki cewa komai dangane da gano wannan kududdufi da ake jefa mutane idan an kashe su a garin Du na Filato.

Ya ce da a garin Musulmi aka samu wannan kududdufi da sun dade da fara surutai da zage-zage a kafafen watsa labarai da kuma shafukan sada zumunta na Intanet. SheiKh Khalid ya roki Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen irin wadannan kashe-kashe na jama’a babu gaira babu dalili.