A gaggauta magance rikicin shugabancin Hukumar NFF – Mustapha Umar

An bayyana cewa  zai fi  kyau a  gaggauta magance rikice-rikicen da ke faruwa  a shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yadda za a baiwa kowane bangare damar  ci gaba da ayyukan bunkasa  wasan kwallon kafa a Nijeriya.Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo , wani kwararre a fannin horar da ‘yan wasan kwallon […]

A gaggauta magance rikicin shugabancin Hukumar NFF – Mustapha Umar
A gaggauta magance rikicin shugabancin Hukumar NFF – Mustapha Umar

An bayyana cewa  zai fi  kyau a  gaggauta magance rikice-rikicen da ke faruwa  a shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta kasa (NFF) ta yadda za a baiwa kowane bangare damar  ci gaba da ayyukan bunkasa  wasan kwallon kafa a Nijeriya.
Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo , wani kwararre a fannin horar da ‘yan wasan kwallon kafa  shi ne ya bayyana haka a ganawarsa da Aminiya, inda ya ce lokaci ya yi da za a samu jituwar dukkanin bangarorin da suke rikici da juna domin tunkarar duk wani kalubale na wasan kwallon kafa a kasar nan.
Ya ce idan aka samu fahimtar juna  ko shakka babu kasar nan za ta yi fice a fannin wasan kwallon kafa, sannan za ta zamo tauraruwa a Nahiyar Afirka  da kuma duniya baki daya idan aka dubi irin yadda muke da ‘yan wasa masu matukar kwazo.
Mustapha Bello Gwarzo ya kuma yi kira ga ‘yan wasan  dake bugawa kasar nan kwallo da su sanya kishin kasa a lokacin da suke kwallo kamar yadda ’yan kwallon wadansu kasashe ke nunawa.
Haka kuma ya yi amfani da wannan dama inda ya shawarci  hukumar kula da wasan  kwallon kafa ta kasa ta sake baiwa Steben Keshi damar sake horar da kungiyar Super Eagles.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa