A gaggauta sakin Bazoum ba tare da bata lokaci ba — Majalisar Dinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bukatar sakin shugaba Bazoum nan take.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin da suka hambarar da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, kuma suke tsare da shi da su gaggauta sakin shi.
Jami’an tsaron Fadar Shugaban Kasar ne, suka tsare Bazoum a Yamai a ranar Laraba, wadanda bayan sa’o’i kadan suka sanar da karbe mulkin kasar.
- Ministocin Tinubu: El-Rufai, Wike, Badaru sun samu shiga
- ’Yan Nijar sun yi casun goyon bayan juyin mulki
“Na yi matukar kaduwa da damuwa game da yunkurin da sojoji suka yi a Nijar kuma na yi Allah-wadai da lamarin. Dole ne a yi duk mai yiwuwa don dawo da tsarin tsarin mulki da bin doka da oda,” in ji babban jami’in kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk a wata sanarwa ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, “Dole ne a gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum ba tare da wani sharadi ba, kuma a tabbatar da tsaronsa. Su ma mambobin gwamnatinsa da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba dole ne a sake su ba tare da wani sharadi ba.
“Ina kira ga duk wadanda ke da hannu da su guji tashin hankali da mutunta hakki da ‘yancin kowa. Yana da kyau a da kiyaye muhimman nasarorin da dimokuradiyya ta samar a ‘yan shekarun nan ga al’ummar Nijar.”
Nijar ta bi sahun kasashen Yammacin Afrika irin su Mali da Burkina Faso da suka fuskanci juyin mulki a baya-bayan nan.