A gaggauta sakin Sowore — Atiku

Hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Nijeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.

A gaggauta sakin Sowore — Atiku

Atiku Abubakar

Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya buƙaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan ƙasar.

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin da ya ce abin kunya ne cin zarafin da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore.

“Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku.

Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya.

Wasu rahotanni ma na bayyana cewa ana zargin ’yan sandan sun lakaɗa wa Sowore duka har ma an ƙarya masa hannu.

Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴa nsanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai ba ne, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Nijeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.

“Don haka muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba,” in ji Atiku.

A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami’an ’yan sanda domin amsa wasu tambayoyi.

A jiya Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ’Yan sanda ya yi masa don ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da zanga-zangar da tsofaffin ’yan sanda suka yi a makon jiya.

Haka kuma, an son Soworen ya bayar da bahasi kan zargin da ya yi na cewa, Babban Sufeton ya kara wa jami’an ’yan sandan da ke aiki a gidansa girma ba bisa ka’ida ba.

Sai dai ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana su a matsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don “dauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton Kayode Egbetokun da kuma hukumar ‘yan sandan ke aikatawa.”

Tuni dai Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar Allah wadai da kamun da aka yi wa Sowore wanda ta ce ya saba wa ‘yancinsa na fadin albakacin baki.

Haka kuma, Amnesty International ta bukaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.