A gaggauta soke karin kudin fetur —NLC

Gwamnati ba ta fara biyan sabon albashin ba, sai ga wannan abin ban tsoro, in ji Ajaero

A gaggauta soke karin kudin fetur —NLC

Shugaban NLC, Joe Ajaero

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira da a gaggauta soke karin farashin man fetur a fadin kasar.

Shugaban NLC na Kasa, Joe Ajaero, ya ce nan gaba shugabancin NLC zai yi taro domin daukar matakan da suka dace kan karin kudin man da na lantarki da kuma mafi karancin albashi.

NLC ta yi wannan kira ne bayan Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) ya bayar da umarnin kara farashin fetur daga N568 – N617 zuwa N855 – N897 kan kowace lita.

NNPC ya musanta bayar da umarnin, gidajen mansa da ke Abuja da wasu wurare sun kara farashin zuwa Naira 897, a Kano kuma N904.

A martaninsa, Ajaero ya ce ba su ji dadin cin amanarsu da karin farashin man fetur da aka yi ba.

Ya ce daga cikin dalilansu na amincewa da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi shi ne alkawarin ba za a kara kudin mai ba, duk da sun san cewa N70,000 ba  zai wadatar ba.

Ajaero ya ce a ganawarsu da Shugaba Tinubu, an ba su zabin mafi karancin albashin N250,000 da karin kudin mai tsakanin N1,500 zuwa N2,000 ko kuma albashin N70,000 babu karin kudin mai.

Ya ce, “Mun zabi na karshen ne saboda ba mu so mu jefa al’ummar kasar nan cikin karin hukunci.

“Amma abin mamaki, bayan wata daya, gwamnati ba ta fara biyan sabon albashin ba, kuma babu wata hujja, sai ga wannan abin ban tsoro mai kama da mafarki.

“Mun gaya wa gwamnati cewa tsarin da ake bi na warware lamarin tallafin man fetur ba shi da kyau kuma ba zai dore ba, amma suka ki ji,” in ji shi.

Ajaero ya koka da cewa duk da tabbacin da shugabannin majalisar dokoki suka ba NLC kan soke karin kudin wutar lantarki, har yanzu ba su yi komai a kai ba.

Ya ce, maimakon regin da aka yi alkawari, sai kara tabarbarewar lamarin ke yi, wanda hakan ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin mawuyacin hali.

Kungiyar NLC ta yi kira da a saki wadanda ake tsare da su saboda halartar zanga-zangar da ta gudana a kwanakin baya.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano