“A Gaida Masallaci:” Martani

Yau kuma na ba makaranta damar su tofa albakacin bakinsu ne dangane da wasikar da muka samu daga masallaci, da fatar mu karasa ibadar wannan wata lafiya.Shafi’u Zakin Ala: Allahumma amin, muna godiya Malam da wannan jan hankali, Allah Ya ba da lada.Abdurrahman Faruk: Kai, Barkallah! Gaskiya Malam ni dai na ma rasa abin cewa, […]

“A Gaida Masallaci:” Martani
“A Gaida Masallaci:” Martani

Yau kuma na ba makaranta damar su tofa albakacin bakinsu ne dangane da wasikar da muka samu daga masallaci, da fatar mu karasa ibadar wannan wata lafiya.
Shafi’u Zakin Ala: Allahumma amin, muna godiya Malam da wannan jan hankali, Allah Ya ba da lada.
Abdurrahman Faruk: Kai, Barkallah! Gaskiya Malam ni dai na ma rasa abin cewa, wallahi gani nake kamar ga ni ga masallatan nan guda biyu yayin da suke hirarsu a kan masallata. Kuma yadda suke rattabo halayen Musulmi sai dai kawai in gyada kai. Allah Ya kara basira.
Muhammad Auwal Badaru: Ka ji wani irin salo! Wai! An gaishe da masu abinsu. Allah Ya sanya mu amfana.
Lawan Muhammad PRP: Madalla! Da wannan nasiha.
Sani Umar Saurayi: Allah Ya sa mu yi koyi da abin da muka ji.
Abdulmajid Usman: Allah Ya kara basira da hazaka
Lawal Ali Reseacher: A wurin masallatan Arewa Sallar mustahabi muka mai da ta ban san wasu kasashen ba.
Muhammad Auwal Ja’afar: Amin! Babu shakka an kai matuka wajen bin hanya ta hikima domin isar da sako mai amfani, muna jinjina ga Shehin Malami. Allah Ya ba mu ikon gyara kura-kuranmu, Ya saka maka da fiyayyen alherinsa, amin.
Sadik Shu’aib: Allah Ya saka da alheri Malam.
Ibrahim S. S. Abdullahi: Malam, da ka tabo batun suturar da ake sa wa a lokacin bikin Sallah ka sosa mini inda yake mini kaikayi. A bara na yi darussa da dalibai (masu hankali) a kan suturar Hausawa jiya da yau. A karshen darussan kusan duk macen da ke wannan ajin ta yi tir da irin halin da muka shiga na bayyana tsiraici da sunan YAYI. A nawa dan karamin tunanin, ina ganin kamar wa’azi muka yi wa juna musamman a wannan aji. Ina da tabbacin duk wanda ke wannan ajin ya fahimci aibin halin da ’ya’yan Hausawa (musamman mata) suke ciki. Ana dawowa hutu sai na rika ganin sababbin (style) na dinke-dinke masu bayyana tsiraici a jikin daliban da suka yi tir da halin da ake ciki. Takaici ya kashe ni. Na rasa inda matsalar take. Lallai akwai bukatar malamai su daddagi wannan lamari. Ina ganin kamar salon wa’azin nawa a aji bai biya bukata ba.
danladi Haruna: Allah Ya kara fasaha Malam.
Mani Kasumawa Kargeri: Masallaci ya yi magana! Muna jin shi.
El-Ameen Daurawa: Masallaci fa ya yi gaskiya. Muna biye Malam.
Abubakar Marke: Lallai kam masallaci ya yi zance mai muhimmanci,ya Allah Ka ba mu abin da mu ma za mu dauki dawainiyar wani ko da guda daya ne kuwa.
Muhammad Salis Jibril: Allah saka wa Malam da alheri, amin.
Rufa’i Surajo: Lallai kam, wannan ya nuna taimaka wa marassa shi, ba sai da azumi ba kamar yadda masu kudinmu suka dauka suke kuma gudanarwa. Fatarmu Allah ba mu ikon ciyarwa saboda Allah.
Maryam Bilyaminu: Fasihin Malami, Allah Ya ba da lada.
Murtala Iliyasu: Fadakarwa ta yi, Allah saka da alheri
Gimba Wazirin Ala: Hazikin masallaci.
Kamalu Muhammad: Masallaci dakin Allah. Ku hidimta wa dakin Allah don samun tagomashi ran gobe.
Mannir Salisu: Hamdan kasiran dayyiban mubarakan fikum.
Umar Jibril: Adabin taimakon al’umma da kuma wayar da kan jama’ar Musulmi. KUKAN KURCIYA…
Abdulmajid Usman: Zantukan fasaha na masu ilimi ne, wane mutum in ji mutuwa!
Bala danhajiya Makarfi: Allah Ya saka da alheri wannan ba karamar matashiya ba ce.
Umar S. Ahmad: Idan na fahimci wannan wasika ce da masallaci ya yi ta da kansa, domin fadakar da masallata da ma masu halin taimakawa, cewa kada wannan kokari nasu ya kasance iya watan Ramadan. Allah Ya biya.
Dauda Adamu: Allah Ya saka Malam, Allah Ka ba mu ikon taimakawa.
Husaini Isiyaku: Farfesa Allah Ya biya, kuma Ya kara basira, amin.
Aminu Mu’azu Zango: Allah Ya kara wa Malam basira da fahimta.
Ali Fasaha Auyo: Maimakon ka ce ka samu wasika a takalminka da ma ka ce za ka yi gargadi ne, amma wannan wasika ai ta yi tsawo tunda ka ce akwai kashi na biyu.
Muhammad Auwal Ja’afar: Allah Ya kara lafiya; ya kuma saka da mafificin alherinSa.
Janare Bature Sahibul-Kalaam: Muna saurare. Abin baiwa ne kai kadai ka gan ta. Ni kam sai na ji karshenta zan yi nawa sharhi.
Salisu Maladi Darazo: Wasu ba su ma fahimci me ake nufi ba. Malam wannan rubutu ka yi shi wancan azumin da ya gabata har abada ba zan taba mantawa da shi ba, ya fito ne a lokacin da ake bukatar irinsa. Allah Ya ba da lada, amin.
Abdulmajid Usman: Hausa sai dan Hausa wane bagwari ya fahimci sakon Malam, ramin kura sai ’ya’yanta! Allah Ya dado basira da hazaka.
Sa’adu Abdu: Allah Ya ja zamanin Shehin Malami.
Shamsu Hamza: Hausa ba dabo ba. Allah Ya kara wa Shehin Malami fasaha, hazaka, basira da fikira.
Kabir Iliyasu Sandamu: Hikima kayan mumini. Allah kara wa Malam basira da hikima, amin.
dahiru Lawal: Ai na san a rina. Allah Ya sanya sakon ya isa ga kunnunwan da aka yi shi, Ya sa kuma a fahimci abin da ya kunsa.
Nana Khadija: ’Yan uwana Allah Ya ba mu ikon bauta masa kuma Ya amsa ibadarmu, amin.
Isma’il Ibrahim: Allah saka da alheri mafi girma.
Kabir Iliyasu Sandamu: Allah gafarta Malam, muna maka barka da shan ruwa tare da godiya bisa nasiha cikin hikima. Allah Ya ba mu ikon gyarawa. Ina maka fatar hutawa lafiya. Mun gode.
Mani Kasumawa Kargeri: Na fara jin abin na danfulani. Wato Malam kamar da ni yake.
Shehu Usman Abubakar: Allah Ya sa mu dace Ya ba mu ikon gyarawa.
Nafisa Muhammad Gada: Haka ne kam Malam, mun gode.
Ibrahim Dalhat: Hikima da fasaha na wurin ma’abuta ilimi. Allah Ya kara maka lafiya da nisan kwana. Allah Ya sa kunnuwa sun ji kuma su aiwatar da gyara a zahirance. Allah Ya ba da lada.
Abdulrazak S. Inuwa: An gaida tunjim bakin aiki. Dattijon arziki Allah saka da alheri.
Aliyu M. Aliyu: Malam muna godiya da wannan tunatarwar, Allah Ya saka da alheri. Da ma Hausawa na cewa kukan kuciya jawabi ne mai hankali shi ke ganewa.
Mabaruka Lawal: Allah Ya kara mana son taimakon ’yan uwa Musulmi, mabukata a kowane lokaci ba a watan Ramadan kawai ba.