A ganina makami ne ya rusa Cocin Synagogue – kwararre a harkar gini
Wani kwararre kan binciken makamai da bam-bamai mai suna Mista Biedomo Iguniewei ya ce rushewar bene hawa shida na cocin synagogue da ke Jihar Legas ya auku ne sakamakon makamin da aka harba wa ginin.Kimanin mutum 116 yawanci ’yan kasar Afirka ta Kudu ne suka mutu yayin da suka ziyarci cocin don yin ibada a […]
Wani kwararre kan binciken makamai da bam-bamai mai suna Mista Biedomo Iguniewei ya ce rushewar bene hawa shida na cocin synagogue da ke Jihar Legas ya auku ne sakamakon makamin da aka harba wa ginin.
Kimanin mutum 116 yawanci ’yan kasar Afirka ta Kudu ne suka mutu yayin da suka ziyarci cocin don yin ibada a ranar 12 ga watan Satumbar bana da muke ciki.
Mista Biedomo dan shekaru 37 da haihuwa wanda ya samu digirinsa na farko a kan binciken kimiyya daga jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno ya shaida wa kotun da ke binciken rushewar ginin a ranar Litinin din da ta gabata cewa ya gano haka saboda kwarewar da yake da ita yayin da ya yi aiki na shekaru shida da masana’antar tsaro ta Najeriya.
Ya ce jirgin da aka ce ya rika yin shawagi a saman ginin jim kadan kafin ya rushe shi ne ya harba makamin mai sanfurin rugugin sinadaran Infrasonic radiation.
Mista Beidomo wanda ya bayyana kansa mai bincike mai zaman kansa ya ce yana yin digirinsa na biyu a fannin bama-bamai a makarantar horar da jami’an sojoji da ke Zariya.
Ya ce saboda kwarewar da ya samu shi ya sa ya yi tattaki tun daga Kaduna ya zo wurin da ginin ya rushe don ya yi bincike kuma ya rubuta sakamakon binciken da ya yi don duniya ta gani.
‘Na ga hoton bidiyon rushewar ginin sai na fara tambayar kaina, me ya janyo ginin ya fadi a kaikaice, bayan na yi bincike mai zurfi sai na gano cewa, an kai wa ginin hari ne daga sama ta hanyar yin amfani da makami na kimiyya wanda kunne dan Adam ba zai iya jin karar sa ba’. In ji shi
Ya ce ‘Su magina za su iya cewa rashin harsashin gini (fandisho) mai inganci da kayan gini marasa kyau ne suke janyo rugujewar gini, amma idan ka je fandishon ginin za ka tarar babu abin da ya same su, ni ina ganin daga sama aka raunata ginin’.
Shi dai shugaban cocin T.B Joshua ya kalubalanci gayyatar da kotun binciken ta yi masa don ya bayar da bahasi.
Sai dai alkalin kotun mai shari’a Lateefa ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Janairun shekarar 2015.