A goya min Ibo

Bahaushe ne da Ibo da Bayarbe suka yi laifi aka yanke musu hukuncin bulala dari-dari. To amma kafin  zartar sai aka ce an ba kowannensu zabi daya na neman sauki. Sai Bahaushe ya ce a dora masa filo a baya kafin a yi masa bulala da aka fara sai filo ya dudduge haka aka karasa […]

A goya min Ibo
A goya min Ibo

Bahaushe ne da Ibo da Bayarbe suka yi laifi aka yanke musu hukuncin bulala dari-dari. To amma kafin  zartar sai aka ce an ba kowannensu zabi daya na neman sauki. Sai Bahaushe ya ce a dora masa filo a baya kafin a yi masa bulala da aka fara sai filo ya dudduge haka aka karasa bulala na shigarsa. Da Ibo ya ga haka sai ya ce a sanya masa filo biyu, shi ma ko rabi ba a yi ba filoli suka dudduge. Da aka zo kan Bayarbe sai aka ce saboda dan kabilarsa ke mulki an ba shi zabi biyu. Sai ya ce, zabi na farko yana rokon a zabi bulalar da ta fi zafi in za a doke shi. Mai yin bulala ya ji mamaki, ya ce masa zabi na biyu fa? Sai ya ce yana son a goya masa dan kabilar Ibon nan a bayansa kafin a yi masa bulalar.
 Daga 09099886988