A guji leka wayar miji —Kwankwaso ga mata
Kwankwaso ya gargadi ‘zawarawa’ da gwamnatin Kano ta yi wa auren gata su nesanci duba wayar abokan zamansu domin a zauna lafiya
Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gargadi ‘zawarawa’ 1,800 da suka ci gajiyar auren gata da gwamantin jihar ta dauki nauyi da su nesanci bincikar wayar abokan zamansu.
A jawabinsa a taron walimar da aka shirya wa sabbin ma’auratan a gidan gwamantin jihar a ranar Asabar, Kwankwaso ya bayyana cewa kawar da kai daga wayar miji daidai yake da guje wa abin da ke kashe aure.
- Yadda kananan yaran Arewa ke gararamba a Kudu da sunan neman kudi
- Gwamnatin Kano ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa duba wayar miji ko ta mata na daga cikin manyan sabubban mace-macen aure, don haka ya shawarce su da su nisanci dabi’ar da ma duk wani abin da ke iya zama kawo matsala ga aurensu.
“An ba ku shawarwari kuma babu iyaka. Malamai, iyalai da dangi da abokan arziki duk su ba ku shawarwari game da yadda za ku zauna lafiya da juna.
“Amma ni ina da wata shawara guda daya; A guji duba wayar miji ko mata. Ku kawar da kai daga wayar abokan zamanku, saboda hakan na daga cikin abubuwan da suka fi haddasa mutuwar aure a wannan zamai,” in ji Kwankwaso.
Tun da farko Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yausu ya bayyana cewa an zabo sabbin ma’auratan ne daga gundumomi 484 da ke fadin kananan hukumomi 44 da ke jihar, daga kowace karamar hukuma aka samu akalla ma’aurata 30.
Ya ce gwamnatin jihar ce ta dauki nauyin auren gaba daya, har da kudin sadaki da kayan dali da kayan gara da kuma jarin N20,00o ga kowace amarya.
A ranar Juma’a aka daura auren, wanda shi ne karon farko bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf.