‘A gyara makarantun ’ya’yan Fulani a Jihar Edo’
Sarkin Fulanin Jihar Neja Alhaji Ardo Isma’ila Rabe wanda ya ziyarci ’yan uwansa Fulani makiyaya na Jihar Edo a makon jiya ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Edo su taimaka wa makarantun ’ya’yan Fulani makiyaya da ke jihar wadanda a cewarsa wasu sun rushe wasu kuma a fili yaran suke daukar darussa.Ardo […]

Sarkin Fulanin Jihar Neja Alhaji Ardo Isma’ila Rabe wanda ya ziyarci ’yan uwansa Fulani makiyaya na Jihar Edo a makon jiya ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Edo su taimaka wa makarantun ’ya’yan Fulani makiyaya da ke jihar wadanda a cewarsa wasu sun rushe wasu kuma a fili yaran suke daukar darussa.
Ardo Isma’ila Rabe ya ce babu wani abin moriya da gwamnati za ta yi wa al’ummar Fulani makiyaya ta burge irin ta ba ’ya’yansu ilimin zamani da na addini “Ban gani wani abin burgewar da gwamnatin kasar nan za ta yi wa Fulani makiyaya da ’ya’yansu ba kamar ta ba su ilimin zamani da na addini. Domin ina ganin babu abin da yake mai da Fulani makiyaya baya a kasar nan illa rashin ilimin zamani da na addini, kuma wannan ya hana su more rayuwa kuma ya mai da su marasa galihu da rayuwarsu ta ta‘allaka kacokan a daji,” inj shi.
Sai ya shawarci iyaye Fulani kan su dage su tura ’ya’yansu makarantun boko da na addini domin samun ci gabansu da zaman lafiya. Kuma ya yi kira ga ardodin Fulani su tashi tsaye su fadakar da jama’arsu muhimmancin ilimin addini da na zamani da kuma zaman lafiya. Ya nuna takaici a kan ci gaba da barnar gonaki da wasu makiyayan ke yi ga manoma, “Ban yi farin ciki da yawan koke-koke kan barnar gonaki da Fulani makiyay ke yi ga manoma ba domin kowa yana dogara ne a kan abin da ya mallaka,” inji shi.