A gyara mana kasuwar lemo ta Kano – Shugban ’Yan lemo

‘Yan kasuwar kayan marmari ta ‘Yan lemo da ke Jihar Kano sun nemi gwamanti ta samar musu da mazubin shara na zamani, tare da gyara musu harabar kasuwar ta hanyar zuba musu interlock, wanda hakan zai magance rashin tsaftar da kasuwar ke fama da ita. Alhaji Muhammadu Umar na Alhaji Alto shi ne Shugaban ‘Yan […]

A gyara mana kasuwar lemo ta Kano – Shugban ’Yan lemo

‘Yan kasuwar kayan marmari ta ‘Yan lemo da ke Jihar Kano sun nemi gwamanti ta samar musu da mazubin shara na zamani, tare da gyara musu harabar kasuwar ta hanyar zuba musu interlock, wanda hakan zai magance rashin tsaftar da kasuwar ke fama da ita.

Alhaji Muhammadu Umar na Alhaji Alto shi ne Shugaban ‘Yan kasuwar Yan lemon a tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana cewa  duk da cewa gwamnatin Jihar Kano tana yin kokari wajen kokarin kwashe shara a koyaushe bukata ta taso, amma akwai bukatar gwamnatin musamman a matakin karamar hukuma da ta samar musu da ma’aikata masu yin shara a cikin kasuwar “idan kun duba kayan da muke sayarwa kaya ne masu tara shara, har ta zama babbar matsalarmu a cikin wanann kasuwa. Alhamdulilliah  gwamnatin jiha na ba mu hadin kai, domin da zarar mun tara shara idan mun sanaar da Hukumar REMASAB, suna zuwa akan lokaci su kwashe, illa dai ’yar matsalar da muke da ita ita ce ta rashin babban abin zuba shara na gwanka, wanda ba zai bar wurin ya yi rami ba, ballantana har a kasa kwashewa. 

Ita kuwa gwamantin karamar hukuma, wacce  ke karbar kaso mafi tsoka na harajin da muke tarawa, muna kira gareta da ta samar mana da ma’aikatan da za su hadu da namu  su rika gudanar da aikin shara a cikin kasuwar nan tamu don tsaftace ta” Inji shi.

Har ila yau shugaban ya bayyana muhimmancin gina musu filin kasuwar da interlock na zamani da suke nema gwmanati ta yi, inda ya ce hakan zai sa kasuwar ta yi tsafta, musamman a lokacin damina. “Idan muka samu aka zamanantar da kasuwa to aka zuba mata daben ‘interlock,’ to na tabbata za mu samu saukin cabewar da kasuwar ke yi, musamman a lokacin damina. Domin idan damina ta zo da cabalbali ba za ki so ki shigo kasuwar nan ba saboda cabi, don haka muke rokon gwmanati da ta yi mana wanann aiki da zai taimaka mana wajen gudanar da sana’armu cikin yanayi na tsafta. Hakan kuma zai taimaka a rika kwashe sharar cikin sauki, domin a wasu lokuta wurin da muke zuba sharar yana yin rami, har ya zama ba a iya kwashe sharar gaba daya” shugaban ya bayyana cewa a bangaren shugabancin kasuwa kungiya tana iya kokarinta wajen tsaftace kasuwa, inda ta dauki ma’aikatan da ke bin sako-sakon kasuwar suna fito da shara tare da tara ta waje guda.

Sannan a cewarsa, kungiyar ta giggina magudanan ruwa don magance ambaliyar ruwa, musamman a lokacin damina. Sai dai shugaban ya yi kira ga gwamnati da masu hannu da shuni da su shigo cikin harkar kayan maramari. Don ceto kayan daga lalacewa “idan lokacin kakar kayan maramari ta zo kamar lokaci irin wanan kayan sukan yi yawa a kasuwa, yadda har za su rika rubewa, don haka muke kira da a samar da kamfanoni da za su rika sarrafa wadanan kayayyaki ana yin lemuna na kwayale ko kuma gwangwani. Haka kuma gwamnati ta samar mana da wasu hanyoyi da za a rika ajiye kayan yadda za su dauki tsawon lokaci ba tare da sun lalace ba. Idan aka yi haka mu an taimake mu, sannan a waje daya an samar wa al’ummar jihar aikin yi , kuma gwamnati a nata bangaren za ta kara samun kudin shiga”

Shugaban na kasuwar ya bayyana cewa farashin kayan marmari abu ne da dillalai masu sayar da kayan a nan ke yin alkalancinsa a tsakaninsu, don haka babu ruwan mai sayar da kaya a ciki. “Kayan marmari kaya ne da yawan samuwarsa ke haifar da arharsa, karancinsa kuma  ke

haifar da tsadarsa. Idan tsadar ta yi yawa takan haifar da rashin ciniki, wanda a gare mu yakan janyo mana asara mai yawan gaske.

Ba a son ranmu kayan ke yin tsada ba yanayin kasuwa ne ke tada farashin kaya. Idan kin duba kayanmu masu saurin lalacewa ne, don haka ba mu son duk wani abu da zai iya janyo mana rashin ciniki, don gudun kada kayanmu su rube. Ya bayyana dalilin da ya sa kayan marmari ke yin arha a lokacin sanyi, inda ya danganta hakan da dalilai biyu, wato yanayi ne da ake yin kakar kayan marmari, haka kuma lokaci ne da jama’a ba su fiye damuwa ko bukatar kayan marmarin ba. “Kasancewar kayan marmari abu ne masu ruwa ba kasafai mutane ke bukatarsu a wannan lokacin ba, haka kuma wannan shi ne lokaci na kakar kayan, ma’ana kayan a cike suke a cikin kasuwa , don haka dole ne su yi arha” 

Haka kuma shugaban ya musanta batun da ake yi cewa ‘yan kasuwar suna tayar da farashin kayan marmari a lokacin azumi, inda ya ce lokaci ne kawai yake zuwa da hakan, amma ba wai da niyya hakan ke faruwa ba.

A karshe cewa ya yi,daga cikin ayyukan da kungiyarsu ke yi sun hada da sulhu a tsakanin ‘yan kasuwa da dillalai da direbobi, sai dai idan abin ya fi karfinta takan tura shi gaban hukuma.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50