A hakan? Allah Ya hana!

Jam’iyyar PDP da shugabanninta da ke matakan gudanar da harkokinta da suka hada da kwamitin zartarwa na kasa da kuma kwamitin amintattu da kungiyar gwamnoninta sun riga Malam tayar da kabbara, domin kuwa sun yi zarbabiyar amincewa da tsayawar takarar Shugaba Goodluck Jonathan, abin da sauran ‘yan Najeriya ke gani a matsayin kasassabar siyasa. Sun […]

A hakan? Allah Ya hana!
A hakan? Allah Ya hana!

Jam’iyyar PDP da shugabanninta da ke matakan gudanar da harkokinta da suka hada da kwamitin zartarwa na kasa da kuma kwamitin amintattu da kungiyar gwamnoninta sun riga Malam tayar da kabbara, domin kuwa sun yi zarbabiyar amincewa da tsayawar takarar Shugaba Goodluck Jonathan, abin da sauran ‘yan Najeriya ke gani a matsayin kasassabar siyasa. Sun amince cewa babu wani dan jam’iyyar PDP, komai nacinsa da kuma farin jininsa ga ‘ya’yan jam’iyya da zai yi jayayya da Shugaba Jonathan a babban taron jam’iyyar don tsayar da dan takarar shugabancin kasa, inda za a yi dakan-daka, shikar-daka don a fitar da Jonathan ba tare da wata hamayya ba.
Wai shin shi Jonathan din ya bayyana masu cewa yana son sake tsayawa takara da bakinsa, ko kuwa su ne ke neman yi masa shigo-shigo-ba-zurfi alhali shi ya san matsalolin da ke gabansa, domin mai sanye da takalmi shi ya san inda ya matse shi, kamar yadda mai daki shi ya san inda yake masa yoyo. Ana iya cewa ke nan uwar jam’iyyar PDP da kuma hamshakan shugabanninta sun fahimci irin wadannan matsalolin da Shugaba Jonathan ke la’akari da su, wadanda kuma suka hana shi fitowa yin rawar gaban hantsi dangane da batun ci gaba da mulki?
To  uwar jam’iyya da gwamnoninta sun kukuta, sun ce ba wani sai Jonathan, anya kuwa hakan ne zai kasance ga sauran ‘ya’yan jam’iyyar da suke ji hakan ya tauye musu hakki, suna kuma da makamin ramuwar gayya a babban ranar da za a raba gardama, lokacin da za a yi zube-ban-kwaryata tsakanin talakawa da wadanda jam’iyyun suka baza don neman mukamai? Bar ta wannan, akwai wadanda suka yi lako, suna jiran Shugaba Jonathan ya furta cewa ya amince da waccan gatar  uwargijin da aka yi masa, zai tsaya zabe, a lokacin ne su kuma za su garzaya kotu don jin ko yana da damar zarcewa, har a rantsar da shi a karo na uku, sabanin ka’idar da kundin tsarin mulki ya gindaya gami da haka. Yanzu dai Shugaba Jonthan ake jira don jin ta bakinsa game da haka, kafin batun amincewar da uwar jam’iyya da gwamnoninta suka yi masa ta fara janyo tashin-tashinar da za ta haddasa babban jidali. Wannan dai ya rage wa uwar jam’iyya, kuma ya kamata ta sani cewa ta yi kitso da kwarkwata, za ta kuma tabbata susa, mai yiwuwa ma sai an tsefe kitson, ko kuma ta yi kundumi, watau ta aske kan gaba daya.
To amma talakawa, musamman ma na Arewa, suna ganin cewa wannan al’amarin bai dada su da kasa ba, amma kuma suna nuna matukar damuwarsu don sun san gwamnatin PDP na iya murda zabe mai zuwa don Jonathan ya haye, ya ci gaba da aiwatar da munanan manufofin da suka sanya ya yi kaurin suna a ciki da wajen kasar nan.  A cikinsu babu wanda zai yarda a ce Shugaba Jonathan zai zarce, a kuma sake shafe wasu shekaru hudu ana fama da munanan matsalolin da suka rigaya suka jefa jama’a cikin kuncin rayuwa da tsananin mayata da tsabar rashin kwanciyar hankali. A yanzu ma yaya lafiyar kura balle ta yi hauka?  Ai shi ke nan sai fitintinun  da aka rigaya aka tayar da sunan addini da kabilanci don daidaita Arewa su gawurta, har su zame garwashin wutar da za ta kone yankin kurmus.
Idan aka yi la’akari da kyau babu wani abin  farin ciki ko wanda zai sa jama’a murna da ya afku a kasar nan tun hawan Jonathan mulki, hasali ma a kullum sai kururuwa ake ta bugawa saboda wahala, ana ta zubar da hawaye saboda jinin bil-adama da ke kwarara a banza,  ko ina sai asara ake ta tafkawa ta ran wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da kuma ta  dukiyar da ke salwanta a banza. Maimakon a ce gwamnatin Jonathan ta tashi haikan wajen kare mutuncin jama’a da tserar da su daga bala’o’in da makiya zaman lafiya ke haddasawa sai ga shi nan kullum al’amura  kara tabarbarewa suke yi tamkar ba gwamnatin da za ta hana, kowacce za ta umurci askarawanta su tsare lafiya da rayukan jama’a, su kuma kare dukiyoyinsu.
Wadannan ba su ke nan ba, an rigaya an rarraba kawunan talakawan Arewa  bisa manufar kabilanci da akidar addini, kuma hakan ya sanya kasar ta rabu gida biyu bisa wannan mummunan yanayin da aka tsire shi da rana tsaka don daure wa Shugaba Jonathan gindi ya kafa gwamnatin da za ta ci gaba da bin wadancan munanan manufofin don kuntata wa wasu jinsin kasar nan.
 Abin takaici game da haka shi ne wasu kabilu da ke bin addini iri guda da na Jonathan sun kasa gane yaudarar da ake yi musu don su nuna goyon baya, ido rufe, gare shi alhali kuwa shi da jama’arsa ba kaunarsu suke yi ba, saboda kasancewarsu ‘yan yankin da ba su kauna, ba kuma za su taba ganin farinsu ba ko da kuwa naman jikinsu za su yi ta yanka suna ba su.
Bisa ga dukkan alamu haka nan za a sake tafiya tare da su, tsananin kishin addini ya rufe musu idanu, ya hana su fahimtar irin mugun halin da aka jefa kasar a ciki, suna nan kuma suna dukufa da ‘yan kanzagin masu wahalar da al’ummomin kasar nan, wadanda kuma suka mayar da su wasu gaso-rogo-a-ba-ka bawo. To wai shin a hakan ne suke so Jonathan ya zarce? Idan kuwa haka ne to, Allah Ya hana!