A hana Fulanin ketare shigowa Najeriya — Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hana Fulanin kasashen waje shigowa Najeriya domin magance matsalar rikicin manoma da makiyaya a kasar. Da yake kaddamar da rukunin gidaje a rugar Fulanin Dansoshiya a Karamar Hukumar Kiru ta jihar a ranar Asabar; Gwamnan ya ce hana makiyaya shigowa Najeriya daga kasashen […]

A hana Fulanin ketare shigowa Najeriya — Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a sa’ilin da yake wasan shadi tare da wasu Fulani a wurin bikin kaddamar da rukunin gidajen rugar Fulani

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta hana Fulanin kasashen waje shigowa Najeriya domin magance matsalar rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Da yake kaddamar da rukunin gidaje a rugar Fulanin Dansoshiya a Karamar Hukumar Kiru ta jihar a ranar Asabar; Gwamnan ya ce hana makiyaya shigowa Najeriya daga kasashen waje ya zama tilas saboda zargin da ake musu na shigowa da makamai da kuma ruruta wutar rikicin makiyaya da manoma.

Gidajen na karkashin shirin jihar Kano na samar wa Fulani makiyaya matsuguni da kuma damar yin kiwo a waje daya maimakon yawo da suke yi a baya.

“Mun yi wannan aiki ne domin dalilai uku: Na farko don mu kawo karshen rikicin manoma da Fulani makiyaya. Dalili na biyu shi ne hana yawace-yawacen makiyaya domin kawo karshen satar shanu.

“Dalili na uku shi ne bunkasa sana’ar kiwo ta hanyar zamanar da ita yadda za a samar da karin madara da nama, domin a zahiri gorar madara ta fi gorar man fetir daraja,” inji Gwamna Ganduje.

Tsarin ya kunshi gina karin gidaje 200 a nan gaba a kan 25 din ya kaddamar kuma aka ba wa Fulani makiyaya  kyauta, a cewarsa.

Gwamnan ya kara da cewa akwai rijiyar burtsatse mai aiki da hasken rana guda biyar, kuma nan gaba za a samar da makaranta da asibiti tare da caji ofis na ‘yan sanda da kuma dam domin samar wa Fulanin ruwan da za su shayar da  dabobbinsu.