A hana tsofaffin gwamnoni zama sanatoci – Farfesa Dadari
Farfesa Salihu Adamu Dadari malami ne a Sashin Bincike da Koyar da Dabarun Aikin Gona, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce ya kamata a kayyade wa’adin ’yan majalisa a Najeriya a dukkan matakai zuwa wa’adi biyu kuma a hana tsofaffin […]
Farfesa Salihu Adamu Dadari malami ne a Sashin Bincike da Koyar da Dabarun Aikin Gona, a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a tattaunawarsa da wakilinmu, ya ce ya kamata a kayyade wa’adin ’yan majalisa a Najeriya a dukkan matakai zuwa wa’adi biyu kuma a hana tsofaffin gwamnoni zuwa Majalisar Dattawa:
A matsayinka na mai sharhi kan al’amarun yau da kullum, yaya kake ganin yanayin siyasar kasar nan?
Najeriya tana tafiya ce da tsarin siyasar kasar Amurka, wanda ko su Amurka ba sa yin abin da suka rubuta, a kundin tsarin mulkinsu. Suna bin tsari ne bisa karfin tattalin arzikin kasarsu. Mu a Najeriya da muka zo maimakon mu dauki dimokuradiyyar da za ta dace da al’adunmu da karfin tattalin arzikinmu, sai muka dauko tsarin Amurka na Jari- Hujja. Kuma kamar yadda na fada ko a Amurka ba sa bin tsarin kamar yadda suka rubuta.
A wannan tsari na Amurka da muke bi, ana kashe wa ’yan majalisunmu makudan kudin da ake warewa a kasafin kudin kasa.
Don haka muna son idan har kasar nan za ta ci gaba, a sake duba kundin tsarin mulkin kasar nan, a gyara wasu dokoki da ba su dace da kasar nan ba. Yanzu ’yan majalisa a Najeriya idan an ce za a taba dokokin da suka shafe su, ba za su yarda ba. Saboda su ne suke yin doka. Don haka ya kamata ’yan Najeriya mu fito kwanmu da kwarkwatarmu mu ce a sake gyara kundin tsarin mulkin Najeriya.
Yanzu a wannan tsari da muke bi idan ka yi Gwamna sai ka zama sanata, ka yi ta zama a wajen, wannan babban kuskure ne. Don ba su ne kadai ’yan Najeriya ba. Ya kamata idan ka yi Gwamna na wa’adi biyu daga nan ka gama, sai ka zama uba ka rika bayar da shawarwari. Kuma ya kamata idan ka yi wa’adi biyu a majalisa, ka koma gefe. Haka ya kamata a yi a Majalisar Dattawa da ta Wakilai da majalisun jihohi.
Haka ya kamata tunda an bai wa Shugaban Kasa da gwamnoni wa’adi biyu, haka ya kamata a bai wa ’yan majalisa a kasar nan. Idan ka gama ka bar wadansu su zo su taka tasu rawar, da haka kasar nan za ta ci gaba.
Kamar yadda ka yi bayani cewa ’yan majalisa ba za su yarda a yi wannan gyara ba, to yaya kake ganin za a yi?
Ba za su yarda ba saboda ba su da gaskiya. Don haka abin da ya kamata a yi shi ne ’yan Najeriya mu fito kwanmu da kwarkwatarmu, mu ce ba mu yarda ba dole sai sun sanya hannu, an gyara wadannan dokoki. Idan ba za su sanya hannu ba, su bar majalisun. Domin ba za a ci gaba da zaluntarmu, muna gani ba.
Me za ka ce kan maganganun da ake yi kan kudin da ake kashe wa tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a matsayin fansho?
Wannan ai damfara ce kawai. Domin akwai wanda ya yi aiki, an ce sai ya shekara 15 sannan za a ba shi fansho. Amma wannan da yake tsari ne nasu na son zuciya, sai suka ce in sun fita a ba su fansho. Bayan wadansu sun tafi sanata. Ya zama za su rika karbar kudi wuri biyu ke nan, wannan ya nuna ba mu shirya ci gaba ba. Wannan bai dace ba, don haka a soke wannan tsari. Akwai wadanda suka yi shekara 30 suna aiki har yau ba a ba su fansho. Amma a ce wanda ya yi shekara 4 ko 8 yana Gwamna, an zo ana ba shi makudan kudi bayan ana zargin wadansunsu sun kwashe kudin jihohinsu sun kai kasashen waje.