A hannun Shekarau da Kwankwaso aka lalata siyasar Kano (I)
Tun a zamanin NEPU da PRP, duniya take yi wa Jihar Kano kallon madubin siyasar Arewacin Najeriya. Marigayi Aminu Kano da Muhammad Abubakar Rimi da danmasanin Kano da sauran magabata, suna cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen daga darajar siyasar Kano a Najeriya.A shekarar 1979, Jihar Kano ta zabi jam’iyyar PRP duk kuwa da […]
Tun a zamanin NEPU da PRP, duniya take yi wa Jihar Kano kallon madubin siyasar Arewacin Najeriya. Marigayi Aminu Kano da Muhammad Abubakar Rimi da danmasanin Kano da sauran magabata, suna cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen daga darajar siyasar Kano a Najeriya.
A shekarar 1979, Jihar Kano ta zabi jam’iyyar PRP duk kuwa da cewa NPN ita ake yayi a Najeriya, kuma ita ce jam’iyyar da ta fi kowace karfi. A shekarar 1983, an juya wa Muhammad Abubakar Rimi baya duk da cewa shi ne yake da mulki, kuma aka zabi Sabo Bakin-Zuwo duk da cewar bai fi Rimin farin jini a karan kansa ko kuma sanin siyasa ba. A wadannan lokuta, duk karfin mulkinka, ba ka isa ka tilasta wa mutane su yi irin siyasar da kake so ba, ko kuma ka murde musu zabe ba. Ire-iren wadannan abubuwa su suka sanya ake sha’awar siyasar Kano, a ko’ina a Arewa, kuma ya sanya ta shahara a fadin Najeriya.
A shekarar 2003, siyasar Jihar Kano ta cigaba da kafa tarihi, inda ta samu karin matsayi daga madubin Arewacin Najeriya zuwa madubin siyasar Najeriya baki daya. Wannan ya biyo bayan zaben Malam Ibrahim Shekarau da kuma faduwar Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. A lokacin, an yi ikirarin cewar Shekarau ya ci zabe alhalin ba shi da ajiyar N100,000, inda ya kayar da Gwamna Kwankwaso mai karfin mulki da kudi da alfarma. Duk Najeriya ba inda aka taba ganin haka a wannan lokacin, kuma bayan yin la’akari da lalcewar al’amuran zabe a karkashin Gwamnatin Shugaba Obasanjo a wannan shekara, an yi ittifakin cewar, babu inda aka gudanar da sahihin zabe a duk Najeriya kamar a Jihar Kano. A wannan shekara, ba wai Gwamna Kwankwaso kadai ba, a’a, ’yan majalisu da dama masu karfin kudi da mulki sun yi asarar kujerunsu. Duk da cewa akwai gagarumin tasirin Janar Buhari a siyasar Kano a wannan lokaci, amma wannan shekara ta 2003 ita ta tabbatar wa duniya cewar siyasar Jihar Kano tana nan daram yadda aka santa duk da lalacewar da siyasar Najeriya ta yi. Wato kudinka ko mulkinka ko magudinka, a Kano, bai isa ya ba ka mulki ba, ba tare da sahhalewar talakawa ba.
Kai, a takaice ma, idan aka ci gaba a haka, to jihohi irin su Oyo da Edo da Imo da Nassarawa da Zamfara za su iya shan gaban Kano ta fuskar ingantacciyar siyasa ta ra’ayi da ’yanci.
Wannan lalacewar da siyasar Kano ta yi ba komai ba ne fa ce laifin tsohon Gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da kuma Gwamna mai ci yanzu, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ko da yake mu kanmu mabiya mun bayar da tamu gudunmawar. Kwankwaso da Shekrau su ne suka share wa magudin zabe wajen zama a Kano, kuma su ne suka assasa al’adar sanya jam’iyya da shugabanninta a cikin aljihu, kowannensu ya yi mulki kuma ya bar tarihi mai kyau daidai iyawarsa. \Ayyukansu sun nuna cewar ba su damu ba dan tarihin siyasar Kano ya lalace in dai ta su siyasar za ta ci gaba da habbaka. A takaice dai, sun lalata tsarin da su suka fi kowa cin moriyarsa a Kano.
Lokacin da Kwankwaso ya zama gwamna a shekarar 1999, babu wani abu na nagarta da alfarma a zahiri wanda Dakta Abdullahi Umar Ganduje bai fi shi ba. Amma saboda tsaftar siyasar Kano a wancan lokaci, ba a murde masa zaben fidda gwani na PDP an bai wa Gandujen ba. A lokacin da jagorancin PDP ya dawo hannun Kwankwaso, a shekarar 2007, shi kadai ya yi fatali da nagartattun ‘yan takara kusan guda bakwai, wadanda suka shiga zabe tare da shi, ya dauki takara ya bai wa Ahmad Garba Bichi.
Idan muka waiwayi Shekarau, a shekarar 2003, tsaftar siyasar Kano na wancan lokaci ta sa aka yarda cewar Ibrahim Little ya karya doka ta hanyar tsayawa takara ba tare da ya ajiye mukaminsa na shugaban jam’iyya ba, kuma ba a kalli kudinsa, yawan jama’arsa ko daurin gindin sa ba, aka karbe takara aka ba shi duk da cewar ba shi da kudi ko wani ubangida a siyasance, kuma ana ganin ma ba zai iya takarar ba. Amma a shekarar 2011, lokacin da jagorancin jam’iyyar ANPP ya ke hannun Shekarau, sai ya jingine matsayinsa na jagora, ya tsaya kai da fata sai an zabi abokinsa Mallam Salihu Sagir Takai, kuma ya dage a kan haka, inda ya yi amfani da dukkan damar da ta ke hannunsa wajen cimma burinsa duk kuwa da cewar mafi yawan ‘yan jam’iyyarsa ta ANPP ba su yarda da zabin nasa ba.
Mallam Amir, Shugaban kungiyar Foundation for Better Initiatibes (FBI), ya rubuto daga Chedi, Karamar Hukumar Dawakin-Tofa, Kano. [email protected]
Amir Abdulazeez Twitter: @AmirAbdulazeez Facebook: https://m.facebook.com/amir.abdulazeez