A haramta acaba a karin hukumomin Legas
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya haramta sana’ar acaba a kananan hukumomi hudu na jihar, kari a kan shida na baya.
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya haramta sana’ar acaba a kananan hukumomi hudu na jihar, kari a kan shida na baya.
Gwamnan ya ce ba gudu, babu ja da baya kan matakin, musamman saboda yadda ’yan acaba ke keta dokokin hanya da shiga ayyukan ta’addanci da kuma yin fashi a hanyoyi.
- Yadda Ake Gasar Kyan Rakuma A Saudiyya
- Yadda ’yan bindiga suka kashe dogarin Shugaban Kamfanin Jirgin Kasa
Da yake sanar da sabon haramcin a kananan hukumomin Kosofe, Oshodi-Isolo, Shomolu da Mushin, gwamnan ya ce, “Muna sa ran wannan matakin zai fara aiki cikin kankanin lokaci, kuma al’umma za su ba mu hadin kai.
“Masu sana’ar da ke wuraren da ba a haramata ba kuma muna shawartar su da su nemi wata sana’ar.
“Muna sa ran masu sana’ar a kananan hukumomi da yankunan da muka zayyana za su bar manyan hanyoyin kafin a fara daukar mataki kansu.”
A ranar 1 ga watan Yunin 2022 ne dokar gwamnan ta haramta sana’ar haya da babura a kananan hukumomin Surelere, Etiosa, Lagos Island, Mainland, da kuma Apapa ta fara aiki.
Fitar da sanarwar ke da wuya, masu sana’ar suka koma sauran wuraren da ba a hana ba, wasu kuma sauka sayar da baburansu suka koma mai kafa uku, da sauransu.
A bangaren mazauna jihar kuwa, sun bayyana mabambantan ra’ayoyi, musamman saboda kasancewar acaba hanyar sufuri mafi farin jini a Legas, da kuma zamowarsa sana’ar talakawa.
Legas dai ba ita ce kadai ta dauki wannan mataki ba, domin jihohi irinsu Kano, sun dade da haramta sana’a, dalilin tsaro.