A haramta daukar fasinjoji a bakin tituna – Najeem Yasin
Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa, Alhaji Najeem Usman Yasin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen gudanar da daukar fasinjoji a bakin titunan kasar nan, kuma ta kafa ginannun tasoshi a yardaddun wurare, domin kare rayukan jama’a. Alhaji Najeem ya yi kiran ne lokacin da yake maida martani a kan tashin bam a tashar mota […]
Shugaban kungiyar Direbobi ta kasa, Alhaji Najeem Usman Yasin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen gudanar da daukar fasinjoji a bakin titunan kasar nan, kuma ta kafa ginannun tasoshi a yardaddun wurare, domin kare rayukan jama’a.
Alhaji Najeem ya yi kiran ne lokacin da yake maida martani a kan tashin bam a tashar mota ta gefen titi da ke Nyanya a yankin Birnin Tarayya Abuja, inda mutane da dama suka rasu, wasu suka yi rauni.
Shugaban ya ce baya ga matsalar masu daukar fasinjoji a gefin titi da yi musu fashi, irin wadannan tashoshin suna kawo cinkoson ababen hawa, wanda hakan babban hadari ne. Ya ce kungiyarsu a shirye take ta hada kai da kananan hukumomi wadanda suke da hurumin gudanar da tashoshin mota wajen zaben wurare da za a yi tashoshi da raya su domin inganta kudin shiga ga gwamnati da kuma samar da zaman lafiya ga kasa.
Alhaji Yasin ya ce kungiyar ta rasa mambobi a yayin tashin bam na Nyanya da wadanda suka samu raunuka da kuma motoci da suka kone a hadarin. Ya bukaci jama’a su fifita shiga mota a tasha, sannan ya bukaci shugabannin tashoshi mota a kasar nan su kara tabbatar da tsaro a tashoshin ta hanyar kawar da motocin da ba sa aiki, kuma su sa’ido a kan mutane da ke hada-hada a tashoshin don tabbatar da tsaro.
Dangane tare-tsaren da kungiyar ke da su don kyautatata wa direbobi da fasinjoji, ya ce akwai tsarin RAIS da suke gudanarwa inda ake bukatar kowane fasinja ya rubuta sunansa da lambar makusancinsa, domin tuntubar danginsa idan wani abu ya bijiro.
Sai kuma Naira dubu 40, da ake bayarwa don jinya idan fasinja ya samu rauni ko a bad a Naira dubu 150 ga iyalansa idan ya rasu a hadari.