‘A haramta wa baki zuwa Borno karatun allo’

Masu ruwa da tsaki sun bakaci a wajabta wa iyayen da ke tura ’ya’yansu makaratun tsangaya su rika kaiwa da abincinsu

‘A haramta wa baki zuwa Borno karatun allo’

Almajirai na karatu a makarantar Allo

Masu ruwa da tsaki kan sake fasalin karatun Tsangaya a Jihar Borno sun bukaci gwamnati ta kama tare da sanya yara masu gararamba a kan tituna a makarantun kwana na musamman.

Sun kuma ba da shawarar wajabta wa iyayen da ’ya’yansu ke zuwa Maiduguri karatun allo daga sassan jihar su rika kai musu kayan abinci.

A taron kwana biyu da suka gudanar a Maiduguri, sun ba da shawarar a kafa cibiyar makarantun tsangaya ta zamani  ta a kowacce daga mazabun Sanatoci uku a matsayin gwaji a jihar.

Mahalarta taron sun kuma nemi a haramta tura yara ’yan kasa da shekara 12 karatun allo daga wasu garuruwan jihar zuwa Maiduguri.

Kazalika sun nemi gwamnati ta ɗauki matakan hana kwararowar almajirai daga jihohi da ƙasashe maƙwabta, tare da tallafa wa makarantun tsangaya da malamansu a jihar.

Sun jaddada muhimmacnin gaggauta kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta kunshi hukumar makarantun tsangaya da Islamiyya da sauran hukumomin tabbatar da doka tare da ba su ikon aiwatar da wadannan matakai.

Hakazalika, duk motocin da ke shigowa Maiduguri ya kamata a tantance su da nufin kama abubuwan laifi, musamman matasa marasa aikin yi.

Sanarwa bayan taron da shugaban hukumar makarantun tsangaya da Islamiyya na jihar, Khalifa Ali A. Abulfatihi, ya sanya wa hannu ta ce  ya kamata a koyar da yaran da ba sa zuwa tsangaya ko makarantun firamare, a ba su horo kan sana’o’i domin kawar da su daga kan tituna.

Sannan ya nemi bai wa hukumar ikon ci gaba da aikin rijistar makarantun tsangaya da Islamiyya da nufin sabunta bayanan dalibai da malamai kafin watan Maris na shekarar 2025.

Sanarwar ta ce gwamnati ta bullo da tsarin da ya dace na shigo da dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da ’yan siyasa da sarakunan gargajiya cikin ayyukan tallafa wa makarantun tsangaya da malamansu tare da jaddada bukatar tallafa wa duk shirye-shiryen tsangaya a jihar.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara