A haramta wa Iran shiga Gasar Kofin Duniya —Ukraine

Ukraine na sahun kasashen da suka rasa gurbi a gasar Kofin Duniya.

A haramta wa Iran shiga Gasar Kofin Duniya —Ukraine

Kofin Duniya

Gwamnatin Ukraine ta roki Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA da ta haramta wa kasar Iran shiga gasar Kofin Duniya da za ta gudanar a Qatar.

Hukumar Kwallon Kafar Ukraine ce dai ta gabatar da wannan bukata dangane da babbar gasar tamaular da za a fara ranar 21 ga watan Nuwamba a kuma karkare a watan gobe.

Bayan wani zama da kwamitin gudanarwa na Hukumar Kwallon Kafar Ukraine ya gudanar ne kasar ta aike wa FIFA bukatar kunshe a wata sanarwa.

Hukumar ta Ukraine dai ta zargi Iran da bai wa Rasha makamai don taimakawa a mamayar da Moscow ke yi wa kasar.

Rokon ya zo kwanaki kadan bayan da Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk Sergei Palkin ya yi kira da a cire Iran, a kuma bai wa Ukraine din damar maye gurbinta a gasar ta bana.

Ukraine na sahun kasashen da suka rasa gurbi a gasar Kofin Duniyar wadda a wannan karon za ta gudana a Gabas ta Tsakiya.

Ita kuwa Iran wadda ta samu gurbin ta ke fuskantar barazanar gaza zuwa gasar musamman bayan zarge-zargen da ke nuna hannunta a taimakon Rasha.