A hukunta da wadanda su kona ofisoshinmu kafin zabe —Shugaban INEC

Taron gaggawan na zuwa ne bayan da aka kone ofishin hukumar da ke jihohin Ogun da Osun a ranar Alhamis, a inda aka kone sama da katunan zabe 65,000 da wasu kayyaki.

A hukunta da wadanda su kona ofisoshinmu kafin zabe —Shugaban INEC

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa  (INEC) ya yi kira da a kamo tare da hukunta duk wadanda aka samu da lafin kona ofisoshinta kafin babban zaben 2023.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin taron tsaro na gaggawa babban ofishin hukumar a ranar Juma’a.

“Wannan hukuma ta damu sosai kan yawan hare-haren da ake kaiwa, ya kamata a kama da kuma dauki kwakkwaran mataki na hukunci (kan masu laifin) yayin da muke tunkarar zabe,” in ji shugaban INEC.

Ya ce, hukumar na daukar matakan gaggawa na gyara ofisoshin nata da aka kona, ta yadda za a fara amfani da su.

Taron gaggawan na zuwa ne bayan da aka kone ofishin hukumar da ke jihohin Ogun da Osun a ranar Alhamis, a inda aka kone sama da katunan zabe 65,000 da wasu kayyaki.