A ina hakoran Kaguwa suke?
Bincike ya nuna kaguwa na rayuwa a doron kasa shekaru miliyan 200 da suka shude
Masana sun ce Kaguwa na daga cikin kwarin da ake lissafa su cikin dangin kifaye.
Kwari ne wadanda suke iya rayuwa a kan tudu da kuma a cikin ruwa.
- Da gaske kafafun shanshani sun kai 100?
- Dorinar ruwa: Dabbar da ke iya rike numfashi tsawon minti 5 a cikin ruwa
Kamar sauran kwari, Kaguwa na da tarin siffofin da suka kebanta da su.
Ga wasu daga ciki kamar yadda masana suka bayyana:
* Akwai nau’ikan Kaguwa sama da 4,500 a duniya.
* Yawancin nau’ukan suna rayuwa ne a yankunan bakin teku mai gishiri.
* Halitta ce wadda ta dade a doron kasa, don kuwa, binciken masana ya nuna kaguwa na doron kasa shekaru miliyan 200 da suka shude.
* Nau’in da ake kira ‘Japanese Spider Crab’, su ne kaguwa mafi girma, tsayinsu kan kai kafa 12. Sannan nau’in ‘Pea Crab’ su ne mafi kankanta, wanda tsayinsu bai wuce inci 0.27 zuwa 0.47 ba.
* Kwari ne masu tafiya gefe da gefe.
* Abubuwan da kaguwa ke ci kuwa sun hada da nama da tsirrai da kananan kwari da sauransu.
* Shirya yin kwai da saka kwan, komai na aukuwa ne tsakanin mako daya zuwa biyu.
* Kaguwa na saka kwayayen da yawansu ya kai 1,000 zuwa 2,000.
* Idan ba a fuskanci wata takura ba daga manyan kwari ko dabbobi, kaguwa na iya rayuwa na tsawon shekara uku zuwa hudu.
* Suna sadarwa a tsakaninsu ne ta samar da wani sauti ta hanyar shafa sassan jikinsu da kafafunsu.
* Wani abin al’ajabi game da kaguwa shi ne, hakoransu a ciki suke. Sannan hannuwan nan biyu da suke da su, da su suke amfani wajen rike abu su kai baki. Haka ma sukan yi amfani da su a matsayin garkuwa don kare kansu daga wata cutarwa.
* Suna da baiwar iya sake toho da duk wani sashen jikinsu da suka rasa.