A ina ’yan Aljanna ke fitsari?

Wani bakauye ne zai je suna wani gari, to a cikin mota sai direba ya sanya kaset din wa’azi, inda wani malami ya yi bayanin ni’imomin da suke cikin gidan Aljanna kowa na jin dadi. Ana cikin haka sai motar ta kwace wa direba ta fadi da su, wadansu suka mutu wadansu suka ji rauni, […]

A ina ’yan Aljanna ke fitsari?
A ina ’yan Aljanna ke fitsari?

Wani bakauye ne zai je suna wani gari, to a cikin mota sai direba ya sanya kaset din wa’azi, inda wani malami ya yi bayanin ni’imomin da suke cikin gidan Aljanna kowa na jin dadi. Ana cikin haka sai motar ta kwace wa direba ta fadi da su, wadansu suka mutu wadansu suka ji rauni, aka kwashe su zuwa asibiti. Bakauyen nan na farfadowa ya bude ido ya ga fankoki suna juyawa, ga silin fari, fenti fari, shimfidun gadajen ma farare, ma’aikata da fararen kaya, duk inda ya duba sai ya ga fari fat! Sai kawai ya dubi na kusa da shi ya ce “Malam don Allah a ina ’yan Aljanna ke fitsari?”
Daga 09092969381