A inganta noma da kiwo da sana’oin hannu (I)
Tun kafin zuwan Turawa aka dogara da noma da kiwo da sana’o’in hannu, har zuwa 1914, inda aka dunkule bangarorin Kudu da Gabas da Yamma aka yi amfani da dukiyar Arewa aka gina kasar baki daya, har da hako man fetur da sauran albarkatun ruwa da na kasa. Bayan an yi wa wasu shugabannin Najeriya […]
Tun kafin zuwan Turawa aka dogara da noma da kiwo da sana’o’in hannu, har zuwa 1914, inda aka dunkule bangarorin Kudu da Gabas da Yamma aka yi amfani da dukiyar Arewa aka gina kasar baki daya, har da hako man fetur da sauran albarkatun ruwa da na kasa. Bayan an yi wa wasu shugabannin Najeriya na farko kisan gilla, musamman ganin an yi watsi da noma da kiwo da sana’o’in hannu, wadanda suka dogara da su, suka tsiyace saboda rashin abin yi, su kuma ba sa amfana da man da ake hakowa, sai dai su ji shugabanni suna sace biliyoyin Naira har da tiriliyoyin Naira, an kasa kwatowa, balle a hukunta su, kamar yadda ake hukunta kananan barayi.
Ta fannin noma ake samar da duk nau’in abinci, da gyada da auduga da karo da kwara da ridi da makamantansu da ake fitar da su ta hanyar Hukumar Sayen Amfanin Gona ana samun kudaden musaya, wadanda aka gina Najeriya da su.
Kuma da kiwo aka rika samar da fatu da kiraga da kaho da kofato da kasusuwa, wadanda aka rika fitar da su zuwa wasu kasashe ana sayarwa, ana samun kudin musaya da aka gina Najeriya da su. Bayan nama da madara da man shanu da cukwi da kindirmo da nono da muke amfani da su a Najeriya.
Sai sana’o’in hannu da suka hada da jima ta bagaruwa da samfera da jaje da kwarno. Ga kuma fatun damisa da cita-rabbi masu gashi, ga kuma fatun mesa, kada da tandara da kasa da maciji da guza da damo da sauransu (Reptiles) da ake jemewa da bagaruwa kurum. Sai kuma sana’o’in hannu na fannin fatu: takalma, jakankuna da matasai da dardumar tsakar daki (carpet) da damarar kugu (belt) da sauransu, wadanda aka yi amfani da su wajen samun kudin musaya da aka gina kasa da su, masu yin sana’ar suka arzurta. Yanzu kusan duk sun mutu, saboda sakacin masu mulki na yanzu.
Rini kuwa, wanda aka san mu da shi tsawon daruruwan shekaru, hatta Firayi Ministar Ingila Margaret Thatcher sai da ta taba zuwa kofar Mata a birnin Kano ta gani da idanuwanta, har ta koka mana a kan duk tsawon shekarun nan babu ci gaba? Yanzu har ’yan China an bari suna shigo da rinannun kaya, suna kashe wa namu kasuwa.
Ba a maganar saka ta zannuwa da luru da gwado da kadin zaren yin saka da aka san tsofaffin mata da mutanen kauye da yin su. Bayan kadin zare da abawa na auduga, duk an manta da su. Sai kira da sassaka da ake amfani da su wajen yin fartanya da garma da sungumin yin shuka da adda da tebur da manjagara da lauje da wukake da sakata da kuba da kyamare da tagogi da gadaje da kujeru da makamantansu, kamar gatari, migirbi, diga, kibiya, mashi, basilla da sauransu. Sai turmi, tabarya da akushi da koshiya da ludayi da koko da kwarya da masaki da buta da zunguru da butar kasa da kula da randa da kwatanniya da bankin kasa da sauran ababen da ake yi da yumbu, ko karfe da itatuwa.
Ga kuma kaba da ake saka faifai, igiya, ragaya, tabarma da kindai da mangala da makamantansu. Maimakon masu mulki su taimaka wajen inganta irin wadannan sana’o’i ta yadda za a ci gaba da yin su ta hanyar zamani a ingance, a wadace, a rika fitar da su wasu kasashe domin samun kudaden musaya, bayan an wadata kasa, maimakon yin almubazzaranci da kudin mai wajen shigo da irin su daga wasu kasashe (sai dai mu yi ta sayen kayan wasu kasashe, mu ba ma yin komai na sayarwa).
Wajibi ne a hada kan makiyaya Fulanin daji a tsara yadda za su killace shanunsu da tumakansu da awakansu, a zamanance yadda za su rika samar da nono da madara da kindirmo da man shanu. Sannan gwamnati ta nada LBA’s da za su rika sayen shanu da tumaki da awaki daga masu bukatar sayarwa, babu cuta babu cutarwa, kamar dai yadda ake sayen gyada da auduga a da.
A ware filaye na yin kananan masana’antu a zamanance, ta hanyar yin amfani da injina masu saukin sarrafawa (Intermediate Technology) kowacce sana’a a ware mata wuri, a hada masu yin ta guda 10 ko 20 ko fiye a sayar musu da injinan bashi, duk abin da suka sana’anta akwai LBA da zai saye nan take, su kuma su rika biyan gwamnati a hankali, daga ribar da suke samu, yadda za su iya biya cikin shekara biyar ko kasa da biyar, komai ya zama mallakarsu, sai su rika biyan gwamnati haraji (zakka) su kuma LBA’s su rika sayarwa a kasashen waje bayan sun wadata kasarmu da kayan da gwamnati ta hana shigo da irin su.
Manoma da ba sa iya shuke gonakinsu, gwamnati ta hada kai da su ta ba su duk abin da suke bukata bashi, sai sun yi girbi LBA’s sun saya, su biya gwamnati adadin abin da ta ranta musu, kamar yadda aka san gwamnati da Hukumar Sayen Amfanin Gona ta da (Marketing Board).