‘A janye masu yi wa Buhari zagon kasa daga majalisa’

Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya nuna damuwarsa bisa yadda wasu daga cikin ’yan majalisa ke neman yin zagon kasa ga kasafin kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika musu. Alhaji Gambo Bababa ya […]

‘A janye masu yi wa Buhari zagon kasa daga majalisa’
‘A janye masu yi wa Buhari zagon kasa daga majalisa’

Wani dan fafutikar tabbatar da adalci a tsakanin al’umma kuma shugaban kungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Shiyyar Bauchi ta Kudu Alhaji Gambo Abdullahi Bababa ya nuna damuwarsa bisa yadda wasu daga cikin ’yan majalisa ke neman yin zagon kasa ga kasafin kudin bana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika musu. Alhaji Gambo Bababa ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da wakilinmu, inda ya ce sama da kashi 85 cikin 100 na ’yan Majalisar Tarayya da sanatoci talakawa sun zabe su ne sakamakon guguwar Buhari a jam’iyyarsa ta APC. “Amma tunda yanzu mun fahimci suna neman zagon kasa ga manufofin Shugaban kasa kowa zai girbi abin da ya shuka a zaben shekara ta 2019 domin yanzu talakawa sun fahimci inda aka dosa,” inji shi.
Alhaji Gambo Bababa ya ce da yawa talakawan kasar nan ba sa iya cin abinci sau uku a rana sakamakon yadda ake fama da talauci da tsadar rayuwa kuma ba sa zargin kowa sai ’yan majalisa da suke neman mayar da batun kasafin kudin abin gagari a zauren majalisar.
Ya bukaci jama’a su fara yunkurin janye duk dan majalisa mai neman zagon kasa ga gwamnatin APC da Shugaban kasa.