A ji tsoron Allah a kafafen sadarwa

Assalamu Alaikum Edita! A yau ina son ku ba ni dama ne domin in yi kira ga ‘yan uwa mata masu amfani da kafofin  sada zumunta irin na zamani kamar su Facebook, Whatspp, Twitter da sauran su, ganin irin yadda wasun su ke baiyana tsiraicin su, wasu kuma matan aure ne amma basa kula da […]

A ji tsoron Allah a kafafen sadarwa

Assalamu Alaikum Edita! A yau ina son ku ba ni dama ne domin in yi kira ga ‘yan uwa mata masu amfani da kafofin  sada zumunta irin na zamani kamar su Facebook, Whatspp, Twitter da sauran su, ganin irin yadda wasun su ke baiyana tsiraicin su, wasu kuma matan aure ne amma basa kula da wannan, sun saki jikin su hulda kawai suke da maza yadda ran su ya so, wasu ‘yanmatan kuma hira suke da samari, ta yadda ran su ya musu, wasu kuma roko suke yi a taimaka musu da kudi su yi wasu lolurori, wasu kuma kati suke tambaya duk fa a Social Media a turo masu, to ya kamata a ce mata ku da ke da mutumci da kima da daraja a idon mutane ku rike

mutumcin ku da ‘kimar ku, amma sai ku dawo kuna roke-roke ?

Wannan ya faru dani da wata da muka hadu da ita a Facebook tana rokona in tura mata kati, na ce haba Malama daga haduwa yau kawai sai na turo maki kati ? Ta ce wai tana so na mu yi soyayya idan har zan turo mata, daga karshe dai na ki tura mata, kuma na ce ban son ta, domin ba na soyayya kwata-kwata a rayuwa ta, daga karshe ta turo min da zagi ta ci min fuska da zarafi a kan naki turo mata da kati. Kuma na ce ba ni sonta, da haka nake kira ga sauran mata ina ba su shawara akan cewa su rika kiyaye aukuwar irin wadannan al’amura. Su kuma rike mutumcinsu kamar yadda ake duban su da shi. 

Lallai ’yan mataku ji tsoron Allah,musamman a daidailokacin da kuke mu’amala da junaku ko sauran al’umma a kafofin sada zumunta na intanet, wato kafofin da suka hada da Facebook da Whatsapp da instagram da makamantansu. Kuma samarin ku ji tsoron Allah mu kyautata mu’amala wajen hulda da juna a irin wadannan kafafe.

A karshe nake rokon Allah Subhanahu wata’alah a kan ya ba ni masoyiya mai so na, wadda za mu dade muna soyayya, har takai mu ga aure!

Actibist Nura Sani Rijau 08108291641/08026664213 Nura sani Rijau <[email protected]>