…..A Jihar Ogun ma an samu wata masana’antar
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Ogun ta gano wani gida da ake tsare da ‘yan mata masu dauke da juna biyu da ake sayar da jariran da suka haifa a kan kudi naira dubu dari 3 kowane jariri daya ga mabukata. ‘Yan sandan sun yi nasarar kama wata mata mai suna Angela Chigoeze da dan uwanta Obinna […]

Rundunar ‘yan Sandan Jihar Ogun ta gano wani gida da ake tsare da ‘yan mata masu dauke da juna biyu da ake sayar da jariran da suka haifa a kan kudi naira dubu dari 3 kowane jariri daya ga mabukata.
‘Yan sandan sun yi nasarar kama wata mata mai suna Angela Chigoeze da dan uwanta Obinna Ndunaga, da suka furta da bakinsu cewa suna biyan kudi naira dubu 70 zuwa 80 ga kowace yarinya da ta haifi jariri a matsayin ladan haihuwa. Wadanda suka yi bari kuma ko suka haifi bakwanni, ba sa samun ko kwabo.
Da yake zagayawa da ‘yan jarida cikin wannan gida da aka mayar da shi masana’antar haihuwar jarirai da ake sayarwa ga mabukata, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Ogun, Mista Ikemefuna Okoye, ya ce, “da misalin karfe 7 na safiyar ranar Alhamis (makon jiya) muka dumfari wannan gida a garin Akute, sai dai ba mu gano komai ba, amma bayan mun samu labari daga baya muka koma muka yi binciken kwakwaf inda muka gano wadannan ‘yan mata kanana masu dauke da juna biyu da aka boye su a cikin babban kambodi (wardrobe) da ake kullewa. daya daga cikin ‘yan matan da aka fito da su daga maboyar, ta fadi kasa a some sai da aka garzaya da ita Asibiti domin farfado da ita. Mun kama wata mata mai suna Angela Chigoeze, wato, ainihin shugabar wannan masana’atar haihuwar jarirai da ake sayarwa, tare da masu taimaka mata, da su kansu
wadannan ‘yan mata su 9, inda muka aika da su sashen bincike na rundunar ‘yan sanda da ke Eleweran, Abeokuta, domin ci gaba da binciken wannan al’amari na rashin imani da tausayi.” Inji Kwamishina Okoye.
Wannan mata Angela Chigoeze, ‘yar asalin jihar Abiya, ta shaida wa manema labarai cewa, mijinta mai suna Emmanuel Chigoeze, wanda ya tsere, shi ne ya karbi hayar wannan gida da ake gudanar da mummunan harkar a cikinsa. Ta ce a bara ne suka fara harkokin magungunan gargajiya a cikin gidan.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da sunayen ‘yan matan da aka kubutar da su kuma ake tsare da su kamar haka: Gift Jeremiah da Blessing Sabiour da Precious Staben da Miracle Eze dukkansu masu shekaru 25 da haihuwa da Joy Okoro da bibian Prncewill masu shekaru 20 da Stella Samuel mai shekaru 19 da Agnes Igbo mai shekaru 22.
Kwamishinan ya kuma nuna matukar farin ciki ga mutanen da suka ba su labarin bullar wannan al’amari. Ya roki jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda wajen ba su labarin da zai kai ga gano maboyar miyagun-iri domin kawar da su daga cikin jama’a.