A jinkirta aiwatar da dokar hana kiwo a Binuwai

A watan nan na Nuwamba ne ake sa ran fara aiki da dokar nan ta hana kiwon dabbobi a Jihar Biniwai. Tun kafin ma a shiga fara aiki da dokar, an yi ta samun sa-toka-sa-katsi tsakanin gwamnatin jihar da kuma Fulani, wadanda kungiyar Miyetti Allah Makiyaya Dabbobi ta Najeriya (MACBAN), reshen Jihar Biniwai. Tuni dai […]

A jinkirta aiwatar da dokar hana kiwo a Binuwai

A watan nan na Nuwamba ne ake sa ran fara aiki da dokar nan ta hana kiwon dabbobi a Jihar Biniwai. Tun kafin ma a shiga fara aiki da dokar, an yi ta samun sa-toka-sa-katsi tsakanin gwamnatin jihar da kuma Fulani, wadanda kungiyar Miyetti Allah Makiyaya Dabbobi ta Najeriya (MACBAN), reshen Jihar Biniwai. Tuni dai Majalisar Dokoki ta kammala dokar, inda shi kuma Gwamna Samuel Ortom ya rattaba mata hannu a watan Mayu da ya gabata, a sakamakon rikice-rikice da aka yi ta samu tsakanin manoma da makiyaya a jihar. Mafi muni daga cikin irin wadannan rikice-rikice, shi ne wanda ya faru a karamar Hukumar Agatu, inda aka rasa rayuka da yawa, dubbai kuma suka rasa muhallansu.

Ita dai dokar, tana ishara ne da hana kiwon dabbobi, yadda ake yawo da su kwararo-kwararo, a maimakon haka dokar ta nemi a rika samar da gonakin kiwo na musamman a wuri daya killatacce. Tun da aka samar da dokar nan aka yi ta samun canjin miyau tsakanin gwamnati da makiyaya na kungiyar Miyetti Allah a jihar. A yayin da ita kungiyar ke neman gwamnati da ta soke aiwatar da dokar, ita kuma gwamnati ta ce babu ja da baya, kasancewar dokar ta samu amsuwa sosai daga al’ummar jihar.

Tun kafin shigowar watan nan na Nuwamba, Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Alhaji Garus Gololo ya ce membobin kungiyarsa za su yi kaura daga jihar. Ya ce ba su da zabi illa su bar jihar “tun da gwamnati ba ta samar da wani shirin inda za su ajiye shanunsu da kiwata su ba.” Ya kara da cewa: “Wannan doka tana da rikitarwa. Sun ce ba korar Fulani suke yi ba daga jihar amma kuma ba su samar da yanayin rayuwar dabbobinmu ba, babu kasuwar cinikin dabbobi. Sun ce mu sayi filaye domin killace dabbobin, amma abin tambayar shi ne, daga wurin wa za mu sayi filayen? Hanyoyin da ake bi a mallaki filaye a Jihar Biniwai suna da tsauri amma duk da haka sun karfafa cewa dole sai mun sayi filaye. Idan ka sayi fili, kana bukatar Takardar Shaidar Mallaka, domin cancantar mallakarta. Shin ta yaya za mu cika dukkan wadannan ka’idoji a cikin wannan kankanen lokaci?

Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Biniwai, Mista Lawrence Onoja Jnr. ya bayyana cewa an ba da isasshen lokaci domin sayen filayen da gina wuraren kiwo ga makiyaya. Ya ce an shirya sayar da filaye tare da sassauta farashin Takardar Shaidar Mallakar Filaye, domin wannan doka ta yawo da dabbobi don kiwo ta samu nasara. Onoja kuma ya ce wannan doka ba ta fada da wata kabila amma an fito da ita ne da nufin kare lafiyar dabbobi kuma dokar ba ta bar ’yan gida na jihar ba da suke da dabbobi.

Kwamishinan ya ce wadanda ba za su iya cika ka’idojin dokar ba suna da zabin su bar jihar. Masu sharhi kan al’amura za su iya cewa dama can ana son korar wasu ne daga jihar. Wasu makiyaya kuma sun yi barazanar cewa za su tattara a wani wuri a Biniwai domin turjiya da duk wanda ya ce zai hana su kiwo. Duk da cewa an kafa wannan doka domin magance rikicin manoma da makiyaya a jihar, kuma dokar na da goyon bayan al’ummar jihar, duk da haka ya dace a ce an yi la’akari da wasu al’amura, domin kada a karkare da korar wasu rukunin al’umma daga jihar.

Ya dace a ce an fito da tsari mai inganci na kasa baki daya, wanda zai kawo karshen yawace-yawacen kiwo da dabboibi, a tsara yadda za a rika killace su a wurare na musamman a wuri daya. Wannan tsari zai yi tasiri idan aka samu hadin kan dukkan rukunnan gwamnatoci uku – tarayya, jiha da karamar hukuma. Don haka muna shawartar Gwamnatin Jihar Binuwai da ta dakatar da wannan doka a yanzu, ta fito da tsare-tsare masu inganci yadda za a yi wa kowa adalci. Ya kamata a yi taka-tsan-tsan domin kauce wa haifar da wani babban rikici cikin al’umma.