A jinkirta batun yin qidaya a 2018
A wani taron manema labarai da ya yi a Abuja, Shugaban Hukumar Yin Qidaya ta Qasa (NPC) Cif Eze Duruhueoma ya ce tuni Hukumarsa ta fara shirin yin qidaya ta qasa (Census) da ake sa ran yi a shekarar 2018. Ya ce hukumarsa ta ware waxansu yankuna ne da za a gudanar da qidaya ta […]
A wani taron manema labarai da ya yi a Abuja, Shugaban Hukumar Yin Qidaya ta Qasa (NPC) Cif Eze Duruhueoma ya ce tuni Hukumarsa ta fara shirin yin qidaya ta qasa (Census) da ake sa ran yi a shekarar 2018. Ya ce hukumarsa ta ware waxansu yankuna ne da za a gudanar da qidaya ta gwaji da ake musu laqabi da (Enumeration Areas (EA).
Shugaban ya ce Hukumarsa tana buqatar kimanin Naira biliyan 200 don gudanar da qidaya a shekarar 2018. Ya ce ana sa ran gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu dawaxansu hukumomi daga qasashen qetare ne za su haxa qarfi da qarfe wajen samar da wannan kuxi don gudanar da qidayar. Ya ce hukumarsa ta kasafta kashe kuxaxen ne daki-daki a tsawon shekara uku. Ya ce an ware wasu kuxi don yin qidayar gwaji sannan wasu kuxin kuma za a kashe su ne yayin yin qidayar ta ainihi, yayin da za a kashe wani vangare na kuxin bayan an gudanar da qidayar.
Shugaban ya qara da cewa, abu ne mai muhimmanci a ware waxansu yankuna a matsayin gwaji kafin a gudanar da qidaya ta qasa, don yin haka ne zai ba hukumar damar sanin qalubale da kuma hanyoyin da suka kamata a bi a wajen gudanar da sahihiyar qidayar mutane da gidaje a faxin qasar nan.
Shugaban ya qara da cewa, za a ware waxansu yankunan da za a yi qidayar ta gwaji ne a xaukacin Jihohi 36 da ke faxin qasar nan da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja. Ya ce hukumar ta zavi qananan hukumomi 74 ne daga cikin 774 da za ta yi gwajin a cikinsu. Sauran qananan hukumomi 700 da suka rage za a cigaba da yi a cikinsu a nan gaba.
Ya ce tuni hukumarsa ta xauki qwararrun ma’aikata kimanin 50 da za su karaxe faxin qasar nan don gudanar da yin qidayar ta gwaji a qananan hukumomin da aka ware. Sai dai shugaban ya ce xaya daga cikin qalubalen da za su iya fuskanta shi ne na watsuwar ’yan gudun hijira. Akan haka ne ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin addini su ba hukumarsa goyon bayan don ganin an samu nasarar gudanar da yin qidayar ta gwaji a cikin nasara.
Gwamnatin Tarayya ta kafa Hukumar yin qidaya (NPC) ta qasa ne a shekarar 1988. Alhakin hukumar ne qidaya ’yan qasa da kuma yawan gidaje don samar da sahihin bayanan da za su riqa taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da ayyukan raya qasa kamar na mutanen da ke raye da kuma waxanda suka rasu. Sannan kundin tsarin mulkin qasar nan na shekarar 1999 a sashe na 153 ne ya amince da kafa wannan hukuma. Najeriya dai ta gudaar da qidaya ne a shekarar 1953 da 1963 da 1973 da 1991 da kuma a 2006.
Abin lura a nan shi ne duk da yake muna buqatar a yi qidayar qasa a shekarar 2018, hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta bi wajen samar da Naira biliyan 200 a wannan lokaci don gudanar da qidayar a nan gizo ke saqar. Idan muka dubi yadda al’amurran tattalin arziki suka tavarvare a qasar nan, da yadda muke buqatar abubuwan more rayuwa da yadda a kullum ake samun labarin yadda masana’antu ke durqushewa da kuma yadda mafi yawan ’yan qasa ke rasa ayyukan yi, na daga cikin dalilan da za su sa a xaga yin qidayar har zuwa wani lokaci.
Kodayake doka ta nuna ana buqatar a riqa yin qidaya ta qasa ne a duk bayan shekara 10 amma ba kasafai hakan ke faruwa a Najeriya ba. Alal misali, bayan an gudanar da yin qidayar qasa a shekarar 1973 wanda daga baya gwamnatin Marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad ta soke, sai da aka shafe shekara 18, (1991) kafin a sake gudanar da wata qidayar. Daga nan kuma sai da aka sake shafe shekaru 15 watau a 2006 kafin a sake yi. To idan aka gudanar a shekarar 2018 zai kasance shekaru 12 kenan daga shekarar 2006 rabon da a yi qidayar ta qasa. Saboda haka ba lallai ne sai an gudanar da ta 2018 ba saboda matsalolin da suka dabaibaye qasar nan. Muna bayar da shawarar ko da za a xauki wasu shekaru masu zuwa, za a iya yin jinkiri don a shawo kan muhimman matsalolin da suka dabaibaye qasar nan, tun da ba wannan ne karo na farko da aka xauki lokaci mai tsawo ba tare da an yi qidayar ba.
Sai dai muna kira ga Hukumar yin qidaya ta qasa (NPC) da kada ta yi qasa a gwiwa wajen cigaba da samar da muhimman bayanan da za su taimakawa gwamnati wajen aiwatar da ayyukanta. Ba yin qidaya ne kaxai hanyar da hukumar za ta bi wajen taimakawa gwamnati ba.
Sannan muna kira ga Hukumar qidayar da ta cire batun yare da na addini a cikin tambayoyin da take yi a yayin qidayar kamar yadda ta cire waxannan tambayoyi a qidayar da aka gudanar a shekarar 2006. Yin haka na da muhimmanci, don waxannan vangarori ne ke sa ake yin aringizo a yayin gudanar da qidayar da aka yi a baya.