A jiya Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin Landan inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Siriya. Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yaqin basas

A jiya Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin Landan inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Siriya.Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yakin basasar kasar, wanda Majalisar dinkin Duniya ta dauki nauyin […]

A jiya Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin Landan inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Siriya. Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yaqin basas
A jiya Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin Landan inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Siriya. Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yaqin basas

A jiya Alhamis ne ake gudanar da wani babban taro a birnin Landan inda za a tara dala biliyan tara domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Siriya.
Ana yin taron ne kwana guda bayan an tashi baram-baram daga wajen wani taro kan yadda za a dakatar da yakin basasar kasar, wanda Majalisar dinkin Duniya ta dauki nauyin gudanar wa.
kasar Birtaniya ta bayyana cewa za ta bayar da gudunmawar Dala biliyan daya da miliyan 800 ga miliyoyin mutanen da rikicin Siriya da na makwabtan kasar ya shafa.
Firaministan Birtaniya, Dabid Cameron, ya ce kashe kudin kan mutanen zai sa su daina yunkurin barin kasar zuwa wasu kasashen  nahiyar Turai.
Ministan Harkokin Wajen kasar Norway, Borge Brende, ya yi gargadin cewa wajibi ne a samu nasara a taron, idan ba haka ba za a fuskanci kalubale mai yawa.
A ranar Talata ne Sarki Abdullah na Jordan ya shaida wa BBC cewa kasarsa ta kai kololuwar kokarinta wajen yawan ‘yan gudun hijirar Siriya da za ta iya karba muddin ba ta samu wani taimako ba.