A kafa dokar hana likitoci yajin aiki – Shugaban Da’awa

Shugaban Kwamitin Da’awa na kasa Malam Lawal Maidoki ya yi tir da yajin aikin da kungiyar Ma’aikatan Lafiya suka shiga don neman gwamnati ta biya su wasu hakkokinsu. Shugaban ya bayyana lamarin da abin da ya saba wa doka da bai kamata a rika shiga cikin lamarin ba domin karantarwar addinin Musulunci ba ta yarda […]

A kafa dokar hana likitoci yajin aiki – Shugaban Da’awa

Shugaban Kwamitin Da’awa na kasa Malam Lawal Maidoki ya yi tir da yajin aikin da kungiyar Ma’aikatan Lafiya suka shiga don neman gwamnati ta biya su wasu hakkokinsu.

Shugaban ya bayyana lamarin da abin da ya saba wa doka da bai kamata a rika shiga cikin lamarin ba domin karantarwar addinin Musulunci ba ta yarda da daukar irin wannan mataki ba.

Malam Lawal Maidoki ya bayyana haka ne a wurin rabon kudin magani da Hukumar Zakka da Wakafi ke bai wa asibitoci da dakunan shan magani don taimaka wa marasa karfi a Jihar Sakkwato.

Shugaban wanda yake shi ne Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar ya ce yajin aikin ba alheri ba ne, “Matakin ba zai taimaki ci gabanmu ba, lamari ne da ya kamata mu yi tir da shi domin ya saba wa karantarwar addininmu, don kawai kana bukatar samun wani ci gaba na duniya sai ka bar al’ummarka a cikin kuncin rashin lafiya da tsananin ciwo, saboda biyayya ga kungiya ka bar umarnin Ubangijinka da zai ba ka sakamako a gobe kiyama bayan kammala aikin duniya. Ya kamata ma’aikatan da suka shiga yajin aiki su yi la’akari marasa lafiya da ba su iya sayen magani da ke asibitoci daban-daban,” inji shi.

Ya ce da zarar an dakatar da kula da wadansu marasa lafiyar za a sanya rayuwarsu a cikin matsala, “Misali akwai marasa lafiya masu tabin hankali babu wanda yake kula da su, in aka sallame saboda yajin aiki za su shiga daji ne da wasu wurare da suke iya hallaka. Hukumarmu tana kula da wata mace mai tabin hankali da ta haifi ’ya’ya biyu. Da kyar muka gano ’yan uwanta a Hadeja kuma sun fada mana ba su da kudin motar da za su zo Sakkwato su koma da ita gida, a haka muka rika kula da ita da tagwayenta, an shiga yajin aiki an ce mu zo mu tafi da ita kuma ba ta warke ba, to ina ake son mu je da ita? Ire-iren wadannan matsaloli da wandanda suka fi su suna nan birjik a asibitocin kasar nan,’ inji Maidoki.

Sai ya yi kira ga Shugaban kasa da Majalisar Dokoki ta Tarayya su samar da wata doka da za ta hana ma’aikatan lafiya shiga yajin aiki kamar yadda aka hana jami’an tsaro, saboda su ma yajin aikinsu yana haifar da tashin hankali da rasa rayuka a kasa.    

Maidoki ya ce hukumar ta raba Naira miliyan 10.45 don a taimaka wa marasa lafiya da ba su da karfi a jihar, kuma kudin sun fito ne daga gwamnatin Sakkwato domin taimaka wa jama’arta.