A kafa hukumar sa ido a kan kudin yakin neman zabe – Barista Eze
An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa wata hukuma da za ta rika sanya ido kan kudin da ’yan takara suke kashewa wajen yakin neman zabe kan mukamai daban-daban. Shugaban Cibiyar Tabbatar da Adalci, wacce a takaice ake kira CSJ, Barista Eze Onyekpere, shi ne ya yi kiran yayin da yake ganawa da manema […]
An yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kafa wata hukuma da za ta rika sanya ido kan kudin da ’yan takara suke kashewa wajen yakin neman zabe kan mukamai daban-daban.
Shugaban Cibiyar Tabbatar da Adalci, wacce a takaice ake kira CSJ, Barista Eze Onyekpere, shi ne ya yi kiran yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce, kafa sabuwar hukumar ya zama wajibi don a yi maganin badakalar da ’yan siyasa ke tafkawa wajen yakin neman zabe.
Ya bayyana cewa, ya kamata gwamnati ta bai wa hukumar karfin ikon kwace duk wata dukiyar da ’yan takara suka yi amafani da ita da ta saba wa doka da oda.
A ganinsa kamata ya yi hukumar ta zama tana da ikon ta nemi karin bayani tare da karbar motoci da jirage da ’yan takarar suka yi amfani da su wajen yakin neman zabe.
Kuma ya ce, ya kamata a bai wa hukumar ikon bincikar ’yan takarar da suka karya dokokin yakin neman zabe.
Ya dage a kan cewa hukumar za ta rika dakatar da duk wani dan takara da ya karya dokokin da aka gindaya na yakin neman zabe.
Onyekpere ya bayyana cewa, hukumar za ta rika tabbatar da ganin cewa ’yan takara sun bi dokar kashe kudi yayin da suke yakin neman zabe.
“Babu shakka kafa hukumar zai yi maganin duk wata badakala da ’yan takara suke yi da jam’iyyunsu wajen yakin neman zabe. Kuma hakan zai sanya su kansu ’yan takarar da jam’iyyun siyasa su yi taka-tsantsan, tare da bin ka’ida wajen kashe kudi yayin yakin neman zabe,” inji shi.
Ya karkare bayanansa da cewa, kudin din tsayawa takara da masu neman takara ke saya, ‘kamata ya yi hukumar zabe ta rika kula da su.’