A kafa Majalisar Malamai guda daya a Najeriya – Sheikh Sulaiman
Daraktan Cibiyar Bunkasa Ilimi da Wayar da kan Jama’a (AWEDI) da ke Jos babban birnin Jihar Filato, Sheikh Muhammad Suleiman ya yi bukac kungiyoyin addinin Musulunci na Najeriya su hadu su kafa, wata babbar majalisar malaman kungiyoyin wadda za ta rika duba abubuwan da suka shifi addinin Musulunci a kasar nan. Sheikh Muhammad Sulaiman ya […]
Daraktan Cibiyar Bunkasa Ilimi da Wayar da kan Jama’a (AWEDI) da ke Jos babban birnin Jihar Filato, Sheikh Muhammad Suleiman ya yi bukac kungiyoyin addinin Musulunci na Najeriya su hadu su kafa, wata babbar majalisar malaman kungiyoyin wadda za ta rika duba abubuwan da suka shifi addinin Musulunci a kasar nan.
Sheikh Muhammad Sulaiman ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron bita, kan sanin hukunce-hukuncen Mazahabar Malikiya da cibiyar ta shirya a makarantar Albayan da Jos.
Sheikh Suleiman ya ce ya wajaba a samu majalisar malamai guda daya a Najeriya, wadda in wani ya kawo wani abu sabo a addini, sai majalisar ta zauna ta tantance abin, ta ga shin yana cikin addini ko baya ciki, idan ba ya cikin addini sai ta dakatar da shi, idan kuma yana ciki sai a ci gaba da amfani da shi. “Idan ba mu yi haka ba, ba za mu fita daga cikin rudun da muke cikin ba. Kowa zai ci gaba da kirkiro kungiya, kuma ya ce duk wanda ba ya ciki ya zama kafiri. Wannan ba addini ba ne ba kuma tsari ba ne mai kyau,” inji shi.
Sai ya yi kira ga al’ummar Musulmi su koma ga malaman zaure da aka watsar, inda mutum zai iya sanya littafi a karanta masa tun daga farko har karshe, a yi masa fassara a yi masa bayani mai gamsarwa. Ya ce “Wannan shi ne tushen ilimi, kuma daga nan sai mutum ya kama hanyar samun ilimi har ya kai ga manyan littattafai ya gane mazabobin da ake magana.”
Sheikh Sulaiman ya ce sun shirya taron bitar ne ga daliban ilimi domin su kara ilimi a kan sanin fikihu na Mazahabar Imam Malik, saboda mafi yawan matasa a yanzu ba su yi karatun zaure da za su fahimci hukunce-hukuncen tsarki da alwala da najasa da makamantansu. “Babbar manufar AWEDI ita ce a fito da irin wadannan fannoni na ilimin addinin Musulunci don mu rage hayaniyar da ake samu a kasa. Domin idan matasa suka sami ilimi na Mazahabar Malikiya wadda ita ce muke bi a yankin Afirka ta Yamma, hakan zai rage matsalolin da ake samu kan yadda wasu suke dauko mana hukunce- hukuncen wasu mazahabobi wadanda basu muke bi ba a wannan yanki.”
A jawabin Sheikh Abdullahi Yahaya Muhammad ‘Yankaba Kano ya ce da ilimi Allah Ya fifita dan adam kan kowace halitta. Ya ce duk wanda yake son duniya ya yi karatu kuma duk wanda yake son Lahira shi ma ya yi karatu. Ya yi kira ga wadanda suka halarci taron su yi amfani da abubuwan da aka koya musu a wajen taron.
Taron bitar wanda aka yi kwana 30 ana gudanarwa, ya samu mahalarta daga jihohin Filato da Nasarawa da Bauchi da Kano da Ribas da sauran wurare masu dama.