A kama Fulani makiyaya da suka kai hari kan manomi
Wasu Fulani makiyaya da ake zargi da kai hari a kan wani manomi sun shiga komar ’yan sanda a Jihar Ogun. A cewar kakakin rudunar ’yan sandan jihar, waɗanda ake zargin, Muhammad Bello dan shekara 40 da Muhammad Momoh ɗan shekara 30, sai Yusha’u Umaru dan shekara 18, sun shiga gonar Ige Orisade da ke […]
Wasu Fulani makiyaya da ake zargi da kai hari a kan wani manomi sun shiga komar ’yan sanda a Jihar Ogun.
A cewar kakakin rudunar ’yan sandan jihar, waɗanda ake zargin, Muhammad Bello dan shekara 40 da Muhammad Momoh ɗan shekara 30, sai Yusha’u Umaru dan shekara 18, sun shiga gonar Ige Orisade da ke Oke Odo da shanunsu, bayan da suka lalata masa amfani gonarsa, da ya nemi jin bahasin haka sai suka lakaɗa masa duka, suka sassare shi, suka bar shi jina-jina.
Bayan da rundunar ’yan sanda ta sami labarin lamarin ne ta kewaye dajin yankin, inda ta kama waɗanda ake zargin tare da bindiga ƙirar AK 49 mai lamba 513 da alburusai 26 da adduna.
Kakakin ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman ragowar waɗanda ake zargin. Haka kuma Kwamishinan ‘yan sanda a jihar ya ba da umarnin tura waɗanda ake zargin zuwa sashen rundunar da ke kula da manyan laifuka da fashi da makami.