A kamo jami’an da suka lakaɗa wa ma’aikaciyar otal duka —Shugaban EFCC
Olukoyede yana tabbatar wa da jama’a cewa EFCC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da kuma mutunta doka.
Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayar da umarnin kama wasu jami’an hukumar biyu da ake zargi sun lakaɗa wa wata ma’aikaciyar Otel ɗin Regional duka a Jihar Legas.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a intanet, an ga jami’an EFCC da suke sanye da kayan gida suna shiga daya daga cikin dakunan otal din.
- ’Yan sanda sun kama masu ƙwacen waya 985 a Kaduna
- Majalisa ta amince a tsawaita wa’adin aiwatar da Kasafin Kuɗin 2023
An ga wata ma’aikaciyar otal ɗin tana ƙoƙarin buɗe ƙofar daga cikin ɗakin lokacin da mutanen suka buɗe ƙofar da ƙarfi.
A cikin bidiyon da aka naɗa ta kyamarar CCTV an ga ɗaya daga cikin jam’ian na EFCC yana marin matar kafin ya umarce ta da ta fice daga ɗakin.
Shugaban EFCC ya ce lamarin ya faru ne a wani samame da aka kai a safiyar Alhamis inda aka yi nasarar kama wasu.
Olokoyede ya ba da umarnin “a yi cikakken bincike kan abin da ya faru gudanar a otal ɗin tare da tabbatar da cewa ladabtar da duk jami’in da aka samu da laifi,” in ji sanarwar.
“Olukoyede yana tabbatar wa da jama’a cewa EFCC za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da kuma mutunta doka.”