A kamo jami’an lafiyar da suka ki karbar mutanen da suka yi hatsari —Zulum

Duk likita ko ma’aikacin lafiya da ya ki duba marasa lafiya ba tare da wani dalili ba, to ya kamata a kore shi nan take,” in ji Zulum.

A kamo jami’an lafiyar da suka ki karbar mutanen da suka yi hatsari —Zulum

Gwamnan Borno, Babagana Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ba da umarnin hukunta ma’aikatan lafiya da ake zargin sun ki kula da wasu mutane da hatsari ya rutsa da su a Asibitin Umaru Shehu Ultra Modern da ke Maiduguri a kan lokaci.

Zulum ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya je sashen jinyar gaggawa na asibitin a bayan ganin wani bidiyo da ke nuna yadda wasu jami’an lafiya a asibitin suka ki karbar  wadanda hatsarin ya rutsa da su, sai da aka kai ruwa rana.

“Dubi yanayin da aka bar marasa lafiyar suna kuka don neman taimako, amma jami’an asibiti suka ƙi sauraron su; don haka  ba za mu ƙyale irin a maimaita irin haka ba.

“Ban ga dalilin da zai sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kan ma’aikatan da suka yi hakan a wannan asibitin ba.

“Duk likita ko ma’aikacin lafiya da ke kin zuwa wurin marasa lafiya ba tare da wani dalili ba, to ya kamata a kore shi ba tare da jinkiri ba,” in ji Zulum.

A yayin da yake jawabi ga ma’aikatan lafiya a asibitin, Zulum ya ce, abin da abin da aka yi wa marasa lafiyan ”rashin mutunci ne kuma ba za mu lamunta ba.”

Ya kara da cewa, “Dole a cikin sa’o’i 24 masu zuwa, hukumar kula da asibitoci da ma’aikatar lafiya su binciki lamarin tare da ladabtar da duk wadanda suke da  hannu wajen kin karbar mutanen da hadarin ya rutsa da su,” in ji shi a asibitin, a ranar Alhamis.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kata zuba jari sosai a fannin kiwon lafiya, ciki har da jin dadin ma’aikatan fannin, don haka ya yi kira gare su da su mayar da hankali wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga majinyata ba tare da nuna bambanci ba.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Tags