A kamo min Bello Turji — Ministan Tsaro

Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa ƙarewa.

A kamo min Bello Turji — Ministan Tsaro

Ministan Tsaro, Muhammed Badaru, ya umarci dakarun Najeriya da su kamo ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji.

Umarnin da Ministan ya bayar a ranar Alhamis ya zo ne makonni uku bayan Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa kwanakin Turji sun kusa ƙarewa.

Yayin da yake jawabi ga sojoji a hedikwatar Runduna ta Daya da ke Gusau, Jihar Zamfara, a ranar Alhamis, Badaru ya kara wa sojoji kwarin gwiwa, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu yana bibiyar ayyukansu a watannin da suka gabata kuma ya ga ci gaba mai kyau.

“Ina da tabbaci daga kwamandan sojoji kuma na ji daɗi, na tabbata za mu cimma burinmu. Kuna shirye ku gama da su? Kuna shirye ku kawo ƙarshensu? Don Allah ku kawo min Turji.”

Badaru ya kai ziyarar Gusau ne da nufin samun bayanan kan yadda ake tafiyar da ayyukan soji a yankin da ‘yan bindiga suka addaba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Ministan ya kai ziyarar ce ga rundunar sojin ta Operation Fansar Yamma domin inganta alaƙar tsaro tsakanin Gwamnatin Zamfara da ta Tarayya.

Ministan Tsaro yayin ziyarar da ya kai Zamfara
Ministan Tsaro tare da Gwamnan Zamfara
Ministan Tsaro da sauran jami’ai yayin ziyarar da ya kai Zamfara
Ministan Tsaro a fadar Gwamnatin Zamfara