A kan bashin kudi matashi ya caka mini kusa a wuya – dan Kasuwa

Dan kasuwar nan da wadansu matasa suka caka masa kusa a wuya ya warke har ma ya yi wa Aminiya karin haske game da yadda lamarin ya faru. dan kasuwar mai suna Alhaji Auwal Awaisu Rimin Gado, ya ce wani lokaci a shekarar 2017 matashin Aminu Auwal wanda makwabcinsa ne a Unguwar dorayi Kano, ya […]

A kan bashin kudi matashi ya caka mini kusa a wuya – dan Kasuwa
A kan bashin kudi matashi ya caka mini kusa a wuya – dan Kasuwa

Dan kasuwar nan da wadansu matasa suka caka masa kusa a wuya ya warke har ma ya yi wa Aminiya karin haske game da yadda lamarin ya faru.

dan kasuwar mai suna Alhaji Auwal Awaisu Rimin Gado, ya ce wani lokaci a shekarar 2017 matashin Aminu Auwal wanda makwabcinsa ne a Unguwar dorayi Kano, ya nemi ya ranta masa Naira dubu 10, inda shi kuma ya karbi takardunsa na makaranta a matsayin jingina. “Sai dai kafin in ba shi na sanya shi ya rubuta takardar yarjejeniya, wacce ya sa hannu a kai, na karbi takardun nasa da takardar yarjejeniyar a cikin ambulan sannan ni kuma na ba shi Naira dubu 10 kamar yadda ya nema,” inji shi.

“Daga nan ban sake jin duriyarsa ba sai ranar Babbar Sallah ya yi mini waya cewa zai zo ya karbi takardunsa, inda ni kuma na tura masa lambar asusuna na banki don ya turo mini kudina. Shiru bai turo ba har ranar Juma’a sai na kira shi ya ce wai bai samu wanda zai turo mini kudin ta waya ba, sai ni kuma na gaya masa cewa ya kawo min tsabar kudin idan zai zo karbar takardunsa. Ya gaya mini cewa zai zo ranar Lahadi, sai na gaya masa cewa ranar zan je Rimin Gado sai ya ce to shi ma zai je Gwarzo a ranar, don haka a kan hanyarsa ta dawowa zai sauka a Rimin Gado ya ba ni kudina ya karbi takardunsa. Jin haka ya sa na zuba takardun a motata don in tafi da su Rimin Gado,” inji shi.

Ya kara da cewa, “A ranar da lamarin ya faru ina Rimin Gado daidai misalin karfe 5:30, sai Aminu ya kira ni ya ce in jira shi zai zo, wani abu ne ya tsare shi a Gwarzo. Bai tashi kirana ba sai misalin karfe 7:00 na dare, muna Sallah tare da wadansu mutane ya kira ni a waya ya ce ya shigo Rimin Gado. Daga nan na je na taho da shi gidana, inda muka shiga cikin gidan. Daga nan ya dauko Naira dubu 9 ya ba ni, ya ce in yi hakuri ya yi amfani da Naira dubu daya. Na ce masa babu komai, na je na dauko masa takardunsa a mota na ba shi. Ya duba ya tabbatar daidai suke. Na juya zan ajiye mabudin motata, sai na ji ya doke ni a ciki ya kuma rike ni kafin, in yi wani kokari sai na ji wani ya shigo cikin gidan ya shake mini wuya. A takaice a nan suka hadu a kaina suka soka mini wannan kusar a wuyana, inda na fadi a wurin. Sannan suka dauki mabudin motar tawa suka tuka suka gudu,” inji shi

Ya kara da cewa “Mutanen da ke wajen gidan ba su san abin da ke faruwa ba sai da suka ga sun fita da motar a guje, wanda ya tabbatar musu ba ni ne a cikin motar ba. Hakan ya sa suka shiga gidan, suka sane ni kwance cikin jini. Daga nan suka dauke ni zuwa Asibitin Murtala a Kano.”

Ya musanta zargin da Aminu ya yi cewa ya soka masa kusar ce saboda ya kare kansa daga kokarin yin lalata da shi da ya yi. “Babu gaskiya a cikin wannan magana ko kadan, domin an fi shekara guda da ya karbi kudina. Da a ce ina da wata bukata a wurinsa to, ai da tun tuni na neme shi. Amma ban taba kiransa a waya ba, sai da ya kira don kansa kamar yadda na yi bayani a baya,” inji shi.

Idan za a iya tunawa, a kawankin baya Aminiya ta rawaito yadda ’yan sanda a  Kano suka kama Aminu da abokinsa Zakariyya a lokacin da suke kokarin shiga Kano da motar dan kasuwar, bayan sun caka masa kusa a wuya.