A kara duba batun shan taba da dangoginta

A shekarar 2014 ce Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta amince da sabuwar doka a kan shan  taba da dangoginta. Wannan dokar ta tanadi tsauraran hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari da tarar Naira miliyan biyar ga wanda ya karya ta a kasar nan, kamar yadda Ministan Lafiya na lokacin, Onyebuchi Chukwu ya bayyana. […]

A kara duba batun shan taba da dangoginta
A kara duba batun shan taba da dangoginta

A shekarar 2014 ce Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta amince da sabuwar doka a kan shan  taba da dangoginta. Wannan dokar ta tanadi tsauraran hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari da tarar Naira miliyan biyar ga wanda ya karya ta a kasar nan, kamar yadda Ministan Lafiya na lokacin, Onyebuchi Chukwu ya bayyana. An hada da batun kare muhalli a tanade-tanaden dokar. “Muna bukatar mu samar da muhalli mai tsabta daga dattin taba ga al’ummar da ba su bukatar taba ko tu’ammali da ita. Don haka za a bayyana wuraren da zai zama haramun a kai taba cikinsu. Za su iya hadawa da wuraren taruwar jama’a ko cikin gida ko waje,” inji Ministan.

Wani abin da muka yi la’akari da shi shi ne, fasakwaurin taba sigari na daya daga cikin matsalolinta a kasar nan, wanda haka ya sanya ta zama gama-gari a ko’ina, don haka kamata ya yi a tsaurara wajen hana samuwarta fiye da shan ta, domin ai sai an same ta ce sannan za a yi amfani da ita. Haka kuma mun yi la’akari da cewa wannan haramtacciyar sana’a ta fasakwaurin taba tana da riba sosai ga masu yin ta, musamman ganin yadda kanana da matsakaitan kasashe ke wahala daga gare ta.

Ana yi fasakwaurin taba sigari ta kan iyakokin Najeriya na jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina, Kano da Jigawa, inda ake shigo da ita daga Libya da Maroko da Masar, a yayin da wata tabar da ake sarrafawa a kasashen China da Turai da Amurka ake shigo da ita kai-tsaye ta tasoshin jirgin ruwan kasar Benin da Togo, zuwa jihohin Ogun da Kwara. Ta hanyar jirgin sama ma ana yin fasakwaurin sigari, inda masu laifin kan wuce ka’idar shigo da sigarin da ta zarce kara 200.

Dokar da ta samar da sassaucin haraji ga masu shigo da taba daga kasashen ketare ta haddasa samar da gurbatacciyar sigari, inda ake samun dillalan tabar suna sayar da ita a manyan biranen Najeriya, kamar dai yadda ake samun gurbatattun magungunan da ake shigo da su daga waje, haka ita ma taba ake samun ta kuma ake sayar da ita da araha. Irin wannan taba, babu shakka tana dauke da gurbatattun sinadarai, masu cutar da lafiya.

Ana samun takaitaccen bayani game da adadin yawan tabar da ake shigowa da ita a kasar nan, balle ma ko an samu, akan dade ba a bayyana lokaci ko ranar da bayanin ya samu ba. An samu bayanin cewa Najeriya na salwantar da Naira biliyan 89.5 a duk shekara a sigarin da ake shigowa da ita ta hanyar fasakwauri zuwa kasar nan. Haka kuma bayani ya nuna cewa kusan mutane miliyan biyar ke zukar taba sigari a kasar nan, inda kuma suke cutar da mutum miliyan 27 ta hanyar hayakinta, kamar yadda aka yi kintace. Abu ne mai wuya a tantance hakikanin wannan adadi, amma dai abu ne da ke nuna cewa lallai al’umma na cutuwa daga sigari, sannan yana nuna mana irin kalubalen da ke gaban hukuma na magance ta.

Wani kalubalen da fasakwaurin sigari ke nunawa shi ne, yadda tsararren laifi ke gudana kuma yake kara hauhawa. Irin wannan laifin, shi ne yake gudana a kasashen Kudancin Amurka, wanda ya kunshi bayar da cin hanci da rashawa ga jami’an hukuma, kamar kuma yadda wani lokaci ake kashe jami’an da zimmar kashe musu gwiwar tunkarar aikinsu.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka sanya hannu a kudirin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da ya danganci al’amuran sigari. Kudirin yana tafiya kafada-da-kafada da dokar da ta danganci sigari ta 1990.

Mu dai a ra’ayinmu, lallai ne a duba cewa duk wani abu da za a yi domin kare lafiyar al’umma shi ya kamata a ba muhimmanci, ba wai irin dimbin dukiyar da za a samu daga harajin sayarwa da tallata ta ba.