A kara fadada filiyen noma a arewa – Dokta Mato Lambar Rimi  

Wani manomi a Ƙaramar Hukumar Rimi ya yi kira ga manoman Jihar Katsina da su ƙara faɗaɗa gonakinsu ta yadda za a ƙara faɗaɗa noman wannan shekara. Dokta Mato Mai Magani na Lambar Rimi shi ya yi kiran kuma ya ce kiran ya zama wajibi bisa lura da irin halin da yankunan da ake noman […]

A kara fadada filiyen noma a arewa – Dokta Mato Lambar Rimi  

Dakta Mato Lambar Rimi

Wani manomi a Ƙaramar Hukumar Rimi ya yi kira ga manoman Jihar Katsina da su ƙara faɗaɗa gonakinsu ta yadda za a ƙara faɗaɗa noman wannan shekara.

Dokta Mato Mai Magani na Lambar Rimi shi ya yi kiran kuma ya ce kiran ya zama wajibi bisa lura da irin halin da yankunan da ake noman suka shiga na batun taɓarɓarewar tsaro. “Kowa yasan yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna da Sabuwa, Ɗandume, Faskari da Ƙanƙara,Ɗanmusa,Safana da Batsari har zuwa Jibiya dake Jihar  Katsina duk sun samu barazanar matsalar tsaro musamman a yankunan da aka fi yin noman wanda baya ga asarar wuraren noman, su kansu manoman anyi asarar su, walau ta rayukansu ko kuma yin gudun hijra domin tsira da rayuwar ba ma ta gonakin ba. Mun ga yadda wasu marassa tunani suka fito suna kamawa tare da kashe bayin Allah haka nan ba tare da sun yi mu su laifin komai ba. Wannan dalilin ya sa dole wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa ba za su  iya yin noman ba. To don maye waɗancan gurabu da aka samu, yana da kyau yankunan da za su samu damar yin noman da su ƙara faɗaɗa gonakinsu a wajen noman wannan shekara. Da yawa akwai gonakin da ake bari suna zama saura, to wannan karon kam ayi amfani da su don kaucewa faɗawa matsalar ƙarancin abinci.” Inji shi.

Manomin ya ja hankalin an-uwansa akan su mayar da hankali a wajen noma kayan abinci irinsu Gero, Dawa, Masara da kuma Shinkafa. Ya ƙara da cewar, “bayan anyi noman, yana da kyau kuma ayi tanadinsu kada ayi saurin kaiwa kasuwa. Su Wake da irinsu ne za a iya kaiwa kasuwar domin samun kuɗin shiga. Sannan bisa ga dukkan alamu za a fara samun ruwan sama da wuri, saboda haka kada manoma su yi soko-soko wajen yin shuka da wuri.”

Dokta Mato sai yayi kira ga gwamnati da cewa tayi ƙoƙarin rabawa manoman taki akan  lokaci ba sai shuka ta wuce lokacin bukatar shi ba. Sannan a riƙa kawo Iri mai kyau kuma a riƙa wayarwa da manoman kai a duk lokacin da aka kawo Irin da aka san basu san shi ba domin yin amfani da shi ta yadda ta dace.

“Kaga a yanzu akwai sabbin irin da ake kawowa, kamar na Wake da Gyaɗa da kuma ita kanta shinkafar, amma rashin sanin yadda za a yi amfani da su sai dai manomi ya zuba a gona su lalace. Kai hatta da shi maganin ƙwarin da ake kawowa, wani sai anyi maka bayanin yadda za ka yi amfani da shi sannan yake yin abin da ake bukata.”

Dangane da batun farashin kayan amfanin gonar da wasu lokuttan kan yi tashin gwabron zabo yayin da wani lokacin sukan faɗi ƙasa, Dokta Mato yace, abin yana danganta ne da yawa da kuma irin bukatuwar jama’a. “Ai gudun kada a samu ƙarancin kayan amfanin gonar ne wanda zai iya haddasa abincin ya tashi ya fi ƙarfin talakka yasa naga yana da kyau mu ƙara kafto fili don yin noman. Kowa yasan dai arewa bamu da abin da ya fi noman a wajenmu.”

Doktan sai yayi roƙo ga masu gonakin da suke barin gonakin ba su nomawa da su bayar koda da sunan haya ga waɗanda za su iya nomawa. “Gaskiyar magana in bamu yi hankali ba,waɗannan tashe-tashen hankullan waɗanda ke tarwatsa gari,suna iya haifar da annobar ƙarancin abinci domin rashin noman da ba a samu damar yi ba a wuraren da ya ta’azzara.” Inji Dokta Mato.