A karo na biyar, Atiku zai sake tsayawa takara a 2023
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin sake tsayawa takara a 2023. Karo na biyar ke nan a jere da Atiku zai tsaya takarar kujera mafi girma a kasar tun da ya fara zawarcinta a shekarar 2007 a karon farko. Adamu Atiku Abubakar wanda da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasar, shi […]
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin sake tsayawa takara a 2023.
Karo na biyar ke nan a jere da Atiku zai tsaya takarar kujera mafi girma a kasar tun da ya fara zawarcinta a shekarar 2007 a karon farko.
Adamu Atiku Abubakar wanda da ne ga tsohon mataimakin shugaban kasar, shi ne ya bayyana hakan a Yola, fadar gwamnatin jihar Adamawa.
Adamu, wanda shi ne Kwamishinan Ayyuka da Makamashi a jihar ya ce kwarewar mahaifin nasa a siyasa ta kusan shekaru 40 ta sa ya dace ya sake neman kujerar.
Ya ce, “A shekarar 2023, mahaifina zai tsaya takarar kujera mafi girma a Najeriya [ta Shugaban Kasa] saboda ya lakanci harkar mulki da siyasar Najeriya na kusan shekaru 40.
“Idan aka yi la’akari da wadannan abubuwan, ina tunanin mahaifin nawa shi ne mafi cancanta da shugabancin a 2023”, in ji Adamu Atiku.
Ya yi wadannan kalaman ne yayin da yake jawabi kan irin nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a ci gaba da bukukuwan cika shekara daya na gwamna Ahmad Fintiri a jihar Adamawa.
Fadi tashin Atiku wajen neman kujerar Shugaban Kasa
A shekara ta 2007, Atiku ya yi takarar shugaban kasar a karkashin tutar jam’iyyar ACN amma ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Marigayi Shugbaba Umaru Musa Yar’Adua.
Hakazalika a shekarar 2011, Atikun ya sha kaye tun a zaben fidda dan takarar jam’iyyar PDP a hannun shugaba mai ci a wancan lokacin, Goodluck Ebele Jonathan.
Daga nan Atikun ya sake neman tsayawa takara a karkashin sabuwar jam’iyyar hadaka ta APC a shekarar 2015. A nan ma ya sake shan kasa a zaben fidda gwani a hannun Muhammadu Buhari.
To sai dai a zaben na shekarar 2019 din da ta gabata, Atikun ya yi nasarar zama dan takarar babbar jam’iyyar hamayya ta PDP inda suka fafata da Shugaba Buhari amma bai kai ga nasara ba.
Abin jira a gani dai shi ne ko a wannan karon hakar Atikun za ta cimma ruwa bayan shafe kimanin shekaru 16 yana hankoron zama shugaban kasa.
Masana da masharhanta da dama na ganin cewa zaben na 2023 zai kasance mai matukar tarihi kuma fafatawar za ta yi zafi, kasancewar a karon farko cikin shekaru 20, za a fafata ba tare da Buhari ba wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na biyu a shekarar.