A karo na farko ba a yi sallar Juma’a ba a Kano
A karo na farko a tarihi an yi fashin sallar Juma’a a birnin Kano, abin da Kanawa da dama suka bayyana a matsayin bakon al’amari. Hakan dai ya faru ne sakamakon ayyana dokar hana fita da gwamnatin jihar Kano ta yi a yunkurinta na hana cutar coronavirus yaduwa. Dokar hana fita: Yadda Kanawa suka takura […]
A karo na farko a tarihi an yi fashin sallar Juma’a a birnin Kano, abin da Kanawa da dama suka bayyana a matsayin bakon al’amari.
Hakan dai ya faru ne sakamakon ayyana dokar hana fita da gwamnatin jihar Kano ta yi a yunkurinta na hana cutar coronavirus yaduwa.
Wani dattijo mai kimanin shekara 80, Alhaji Bashir Garba, ya ce a iya rayuwarsa bai taba ganin hakan ba.
“Ban taba ganin lokacin da aka ce ba a yi sallar Juma’a ba. Lamarin babu dadi sai dai babu yadda mutum zai yi sai hakuri, tun da hukuma ce ta yi umarni da hakan kuma sha’ani ne na kula da lafiya”, inji Alhaji Bashir.
Shi ma Dokta Yahaya Tanko ya bayyana cewa bai taba ganin lokaci makamancin wannan ba a iya tsawon rayuwarsa ta shekara 71.
Sai dai Shugaban Sashen Tarihi na Kwalejin Shari’ar Musulunci ta Aminu Kano, Malam Kamal Muhammad, ya ce ko da yake a tarihi ba a taba samun lokacin da gwamnati ta hana sallar Juma’a a birnin Kano ba, an taba samun yanayin da aka gudanar da sallar a tsorace wanda ya janyo mutane ba su fita ba.
“A shekarar 1953 a lokacin da aka yi wata rigima ta NEPU da NPC an yi wata hatsaniya da ake kira Kano Riot, wadda ta janyo ba a yi Sallar Juma’a kamar yadda aka saba ba saboda mutane da yawa ba su halarci sallar ba suna jin tsoron yiwuwar barkewar rigima.
“Amma fa ba wai gwamnati ce ta yi umarnin hana fitowa sallar ba”. inji Malam Kamal.
Da karfe 10 na daren Alhamis ne dai dokar hana fitar da gwamanti jihar Kano ta kafa ta fara aiki, lamarin da ya sa ba a fita zuwa masallatan Juma’a ba.
A kasa da mako guda ne dai aka tabbatar da cewa mutane 21 sun kamu da cutar ta coronavirus a jihar Kano.